Yan Brazil ƴan asalin Najeriya
Dan Najeriya dan Brazil (Portuguese) ɗan ƙasar Brazil ne mai cikakken, ko galibin zuriyar Najeriya, ko kuma haifaffen Najeriya da ke zaune a Brazil.
Afuwa
gyara sasheSama da ƴan Najeriya 90,000 da ke zaune ba bisa ka’ida ba a Brazil ba tare da cikakkun takardu ba kafin 1 ga Fabrairu, 2019 za su amfana daga tayin afuwan da gwamnatin Brazil ta yi. Jakadan Najeriya a Brazil, Kayode Garrick ne ya bayyana haka ga Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Brazil. Garrick, ya ce sama da ƴan Najeriya 2,000 da za su ci gajiyar sanarwar afuwa ta Brazil na daga cikin ƴan Najeriya 5,000 da ke zaune a ƙasar a halin yanzu. A watan Satumba na 2008, gwamnatin Najeriya ta buɗe gidan Casa da Nigeria ko "Gidan Al'adun Najeriya" a unguwar tarihi mai suna Pelourinho na Salvador, Bahia, tare da goyon bayan gwamnatocin Bahia da Brazil.
Matsalar wariyar launin fata, 2011
gyara sasheWani batu na kyamar baki / wariyar launin fata da wani malamin jami'a ya yi wa wani ɗalibi ɗan Najeriya a Jami'ar Tarayya ta Maranhão ya girgiza ƙasar a tsakiyar Shekara ta 2011.[1] Daga baya dubban dalibai ne suka sanya hannu kan takardar korar Farfesan.[2]
Duba kuma
gyara sasheManazarta
gyara sashe- ↑ "Nigerian student says he will not go back to Africa, after polemics about racism" (in Harshen Potugis). São Paulo: G1. Retrieved 23 March 2012.
- ↑ "Students ask for dismissal of a teacher suspected of racism in Maranhão" (in Harshen Potugis). G1. Retrieved 23 March 2012.