Yakubu Dogara
Yakubu Dogara CFR[1] (an haife shi a ranar 26 ga watan Satumban shekara ta alif 1967). Ya kasan ce ɗan Najeriya kuma ɗan siyasa,[2] Ya kasance lauya yayinda daga bisani ya zama sipika a majalisar tarayyan Najeriya na goma sha hudu (14) daga shekara ta 2015-2019.[3] Da farko Dogara ya kasance dan jam'iyyar PDP a matsayin dan majalisa mai wakiltar mazabar Bogoro/Dass/Tafawa Balewa ta Jihar Bauchi. Daga bisani ya koma jamiyyar All Progressives Congress (APC).[4]
Yakubu Dogara | |||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
11 ga Yuni, 2019 -
9 ga Yuni, 2015 - 9 ga Yuni, 2019
6 ga Yuni, 2015 -
6 ga Yuni, 2011 -
5 ga Yuni, 2007 - 6 ga Yuni, 2011 | |||||||||||
Rayuwa | |||||||||||
Haihuwa | 26 Disamba 1967 (56 shekaru) | ||||||||||
ƙasa | Najeriya | ||||||||||
Karatu | |||||||||||
Makaranta | Jami'ar, Jos | ||||||||||
Sana'a | |||||||||||
Sana'a | Lauya da ɗan siyasa | ||||||||||
Imani | |||||||||||
Jam'iyar siyasa | Peoples Democratic Party | ||||||||||
yakubudogara.com.ng |
Rayuwa
gyara sasheAn haifi Dogara daga ahalin Yakubu Ganawuri da Saratu Yakubu dogara a shekara ta alif 1967,ranar 26 ga watan Disamba.
Ya fara makarantar Firamare aji 6 a Gwarangah primary School a shekara ta alif 1976. A wancan karamar hukumar Tafawa Balewa na jihar Bauchi.[5]
Karatu
gyara sasheDogara Yayi Makarantar Firamare Gwarangah Primary School, Tafawa Balewa L.G.A a jihar Bauchi. A Shekarar 1975. Daga bisani yayi Bauchi Teachers College a Shekarar 1982. Inda ya tafi jamiar Jos, Plateau State, inda ya samu digirinsa na lauya. A shekara ta alif 1992. Daga shekara ta alif 1992 zuwa 1993 yayi makarantar samun shaidan zama lauya a jihar legas.
An kirashi zuwa Bar a shekara ta alif 1993. Inda daga baya yayi mastas dinsa a Robert Gordon University Aberdeen Scotland.
Manazarta
gyara sashe- ↑ "FULL LIST: Okonjo-Iweala, Abba Kyari... FG nominates 437 persons for national honours". TheCable (in Turanci). 2022-10-02. Retrieved 2022-10-13.
- ↑ https://www.today.ng/topic/yakubu-dogara
- ↑ "Yakubu Dogara at 50". The Sun Nigeria. 2017-12-26. Retrieved 2022-03-02.
- ↑ "Dogara: I'm unaware my traditional title is suspended". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News. 2022-01-26. Retrieved 2022-02-21.
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2015-09-24. Retrieved 2021-05-09.