Yakine Said M'Madi
Yakine Said M'Madi (an haife shi a ranar 11 ga watan Maris 2004) ƙwararren ɗan ƙwallon ƙafa ne wanda ke taka leda a matsayin ɗan wasan baya na kulob ɗin Olympique de Marseille. An haife shi a Faransa, yana buga wa tawagar kasar Comoros wasa.
Yakine Said M'Madi | |||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||
Haihuwa | Marseille, 11 ga Maris, 2004 (20 shekaru) | ||||||||||||||||||
ƙasa |
Komoros Faransa | ||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||
|
Sana'a
gyara sasheSaid M'Madi samfurin matasa ne na makarantun Burel FC da Marseille An haɓaka shi zuwa Marseille reserves a lokacin 2021 – 22 a kakar Championnat National 2. A ranar 7 ga watan Afrilu 2022, ya fito a matsayin ɗan benci ga babban gefe a wasan UEFA Europa Conference League a wasan da kungiyar Girka PAOK FC. [1] Ya sanya hannu kan kwantiraginsa na ƙwararru na farko da ƙungiyar a ranar 13 ga watan Yuli 2022, har zuwa 2024.[2]
Ayyukan kasa da kasa
gyara sasheAn haife shi a Réunion, Faransa, Attoumani asalin Comorian ne. An kira shi zuwa rukunin farko na Comoros U20 a gasar Maurice Revello na 2022.[3] An kira shi zuwa babban tawagar kasar Comoros don wasan sada zumunci a watan Satumba 2022.[4] Ya buga wasansa na farko da Comoros 1-0 a wasan sada zumunci da Tunisia a ranar 22 ga watan Satumba 2022. [5]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "OM-PAOK : le groupe olympien sans Luan Peres et Milik, première pour Said M'Madi" . LaProvence.com . April 6, 2022.
- ↑ Phocéen, Le (July 13, 2022). "OM : M'Madi resigne finalement avec l'OM..." Le Phocéen.
- ↑ Phocéen, Le (May 28, 2022). "OM : déception pour un jeune défenseur marseillais" . Le Phocéen.
- ↑ Lantheaume, Romain (September 16, 2022). "Comores : deux nouveaux de l'OM dans la liste pour la Tunisie et le Burkina Faso" . Afrik-Foot .
- ↑ Houssamdine, Boina (September 22, 2022). "Les Comores s'inclinent en amical contre la Tunisie" .