YNaija

Mujallar yanar gizo ta Najeriya

YNaija dandamali ne na wallafe-wallafe a yanar gizo a Najeriya, wanda Chude Jideonwo da Adebola Williams na ƙungiyar kamfanin watsa labarai na RED Africa suka kafa. An ƙaddamar da YNaija a watan Mayu 2010 tare da masu rubutun ra'ayin yanar gizo da majiyoyin labarai daban-daban. Ana wallafa labarai, da suka shafi siyasa, kasuwanci, nishaɗi, muhalli, fasaha, shahararrun kafofin watsa labaru, salon rayuwa, al'adu, wasan ban dariya da rayuwar kiwon lafiya.

YNaija
URL (en) Fassara http://www.ynaija.com/ da http://ynaija.com
Iri yanar gizo
Service entry (en) Fassara 2010
Alexa rank (en) Fassara 57,569 (30 Nuwamba, 2017)
Twitter YNaija
Facebook YNaija
Instagram ynaija

A cikin watan Yuli 2012, YNaija ta kasance a mataki na #5 a cikin jerin mafiya girma a fannin bulogi a cikin ƙasar, wanda CPAfrica ta fitar da rahoton jerin sunayen.[1]

Alamar tambarin Y! ya ƙunshi shirin talabijin, da rediyo da mujallar da ake bugawa.[2] Jaridar, Y! , bugu ne na kowane wata mai shafuka 100-150 wanda aka soma fara wallafa labarai ta hanayar.

An shirya abubuwan da suka hada da maudu'in #Hashtag Party a watan Yuli 2011,[3][4][5][6] da YNaija Black Ball, da sauransu.

Masu ba da gudummawa

gyara sashe

Ebuka Obi-Uchendu, Tolu Ogunlesi, Kathleen Ndongmo, Japheth J. Omojuwa, Ayo Sogunro da Akintunde Oyebode, akwai wasu masu ba da gudummawa da yawa ga Y! Politico, SuperBlogger da 30 Days, 30 Voices series da wasu jaridu da suka haɗa da; Abang Mercy, Subomi Plumptre[7] da Ifeanyi Dike Jr.

A cikin 2012, wasu daga cikin waɗanda suka kafa YNaija, Chude Jideonwo da Adebola Williams na cikin jerin mutane 40 da mujallar BusinessDay, ta fitar na waɗanda za'a bawa kyaututtuka.[8]

A cikin Fabrairun 2013, Jideonwo da Williams sun kasance suna cikin Forbes 30 Under 30: Mafi kyawun Matasan 'Yan Kasuwa na Afirka.[9]

Shafin yanar gizo na fasaha da salon rayuwa na Najeriya, CPAfrica ta ayyana YNaija a mataki na #5 na (Nigerian blog of the year), a shekara ta 2012.[1][10]

Manazarta

gyara sashe
  1. 1.0 1.1 "Top Nigerian Bloggers 2012" Archived 2017-10-31 at the Wayback Machine, CP Africa.
  2. "Y!TV LAUNCHES EXCITING NEW SHOW, 'EXPLORING' ON ONTV!". YNaija.com. 2016-03-14. Retrieved 2018-03-14.
  3. "The first ever Ynaija Hashtag party…. Pause, Tweet, Play." Olorisupergal.com. 12 July 2011. Archived from the original on 2014-04-13. Retrieved 2013-04-15.
  4. "YNaija + Choc City = #Hashtag – Photos from debut #Hashtag event". Bella Naija. 2011-07-30. Retrieved 2013-04-15.
  5. "YNaija & Chocolate City presents #Hashtag "Pause. Tweet. Play" – Hosted by Denrele, Oreka Godis & Andre Blaze". Bella Naija. 2011-07-19. Retrieved 2013-04-15.
  6. "YNaija #Hashtag Party! See photos of the Very Stylish Fashion & Entertainment Crowd - OnoBello.com: Latest in Fashion, Beauty, News, Features and Events". OnoBello.com. Archived from the original on 2013-04-26. Retrieved 2013-04-15.
  7. "Subomi plumtre (Ynaila)". Ynaija. 19 April 2019. Retrieved 17 January 2020 – via ynaija.com.
  8. "40 UNDER 40: Chude Jideonwu, 27, and Adebola Williams, 26". BusinessDay. September 28, 2012. Retrieved 2013-01-04.
  9. "30 Under 30: Africa's Best Young Entrepreneurs". Forbes. 2012-04-18. Retrieved 2013-04-15.
  10. Folusho (January 11, 2013). "Latest: Top Nigerian Bloggers 2013". Flameville.com. Retrieved 2013-04-15.

Hanyoyin haɗi na waje

gyara sashe