William Mugeyi (an haife shi a shekara ta 1969) ɗan wasan ƙwallon ƙafa ta ƙasar Zimbabwe wanda ya buga wasa a kulob ɗin Bush Bucks ta ƙarshe a Afirka ta Kudu. Tagwaye ne ga ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Zimbabwe Wilfred Mugeyi.

William Mugeyi
Rayuwa
Haihuwa Harare, 4 ga Yuli, 1969 (55 shekaru)
ƙasa Zimbabwe
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
Bush Bucks F.C. (en) Fassara1993-200537628
 
Muƙami ko ƙwarewa Mai buga baya

An haife shi a Salisbury ( Harare), Mugeyi ya buga wasan ƙwallon ƙafa na tsawon shekara 13, mafi yawan wasan sa yana taka leda a matsayin ɗan wasan gefen hagu tare da ɗan' uwansa a rukunin Premier na Afirka ta Kudu tare da Umtata Bush Bucks.[1] [2] Ya lashe gasar Zimbabwe da Black Aces a shekarar ta alif ɗari tara da casa'in da biyu1992 kafin ya koma Afirka ta Kudu tare da Bush Bucks a shekarar 1993. [3]

Mugeyi ya bayyana a wasanni da yawa ga tawagar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Zimbabwe, [4] gami da wasannin share fage na gasar cin kofin duniya na FIFA goma sha biyu. [5] Ya taimakawa Zimbabwe lashe kofin COSAFA a shekara ta 2000, inda ya zura kwallaye biyu a wasan karshe da Lesotho.

Manazarta

gyara sashe
  1. "Mugeyi Retires" . The Herald. 14 June 2005.
  2. Standard, The. "The untold story of Mugeyi twins" . The Standard . Retrieved 2 March 2023.
  3. "Best of the Best – William Mugeyi" . The Zimbabwean. 16 October 2012.Empty citation (help)
  4. William Mugeyi at National-Football-Teams.com
  5. William MugeyiFIFA competition record