Véro Tshanda Beya Mputu
Véronique Tshanda Beya Mputu 'yar Kwango ce. Ta lashe lambar yabo ta Kwalejin Fina-Finan Afirka don wasa mafi kyau a Matsayin Jagora ta hanyar taka rawa amatsayin Felicite.
Véro Tshanda Beya Mputu | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Kinshasa, 20 century |
ƙasa | Jamhuriyar dimokuradiyya Kwango |
Sana'a | |
Sana'a | jarumi |
Kyaututtuka | |
IMDb | nm8644854 |
Wannan mukalar bata da Reference (Manazarta) ko daya, ka taimaka ta hanyar samar da Manazarta daga littafi ko yanar gizo, duba wannan shafin domin samun masaniya akan yanda zaka samar da Reference (Manazarta) a cikin wannan mukalar.
. |
Rayuwar farko
gyara sasheAn haifi Mputu kuma ta girma a Kinshasa, babban birnin Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo .
Ayyuka
gyara sasheA cikin 2017, ta yi fice amatsayin Felicite, wanda aka nuna a bikin Fim na Kasa da Kasa na 67 a Berlin . Da take bayyana rawar da ta taka, ta bayyana cewa ta yi farin ciki game da batun taka rawa wanda ke nuna mata a matsayin masu dogaro da kai ba tare da dogaro da maza don samun abin yi ba. Ta lashe kyautar 'yar wasa mafi kyawu a bikin ba da lambar yabo ta Kwalejin Fim ta Afrika karo na 13 a Legas, Najeriya. An kuma gabatar da fim din a matsayin shigar Senegal ga lambar yabo ta 90 na Kwalejin, wanda ya zama fim na farko daga kasar da aka gabatar a tarihin bikin bayar da kyautar. Jaridar Times ta lura da rawar da ta taka a fim din a matsayin wani babbar jigo na fim din, inda ta bayyana hakan a matsayin "jarumtaka kuma ta ci lambar yabo".
An ba da rahoton cewa sai da tayi fitowa sau huɗu kafin ta shawo kan darakta, Alain Gomis, wanda ba ya son ba ta matsayin.
Manazarta
gyara sasheHaɗin waje
gyara sashe- Véro Tshanda Beya Mputu on IMDb