Uwemedimo Nwoko
Uwemedimo Nwoko listenⓘ (an haife shi a ranar ashirin da bakwai 27 ga watan Oktoba, alif dubu daya da dari tara da sittin da hudu 1964). Lauya ne a Najeriya, ɗan siyasa, Mai fafutukar kare hakkin dan adam kuma tsohon Babban Lauyan da Kwamishinan Shari'a a Jihar Akwa Ibom . [1] [2][3]
Uwemedimo Nwoko | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Ika (Nijeriya), 27 Oktoba 1964 (60 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Karatu | |
Makaranta | Jami'ar Calabar |
Sana'a | |
Sana'a | Mai kare ƴancin ɗan'adam |
Employers | Ma'aikatar Shari'a ta Jihar Akwa Ibom (ga Janairu, 2015 - ga Janairu, 2021) |
Imani | |
Jam'iyar siyasa | Peoples Democratic Party |
Rayuwa ta farko da ilimi
gyara sasheAn haifi Nwoko a ranar ashirin da bakwai ga watan Oktoba, alif dubu daya da dari tara da sittin da hudu wato 1964 a Abiakana, a cikin Karamar Hukumar Ika ta Jihar Akwa Ibom . [4]
A shekara ta dubu daya da dari tara da sab'in da biyu wato 1972, Nwoko ya fara halartar Makarantar Kungiyar Qua Iboe Church (QIC), Ikot Osukpong, Ika LGA na Jihar Akwa Ibom kuma ya bar makarantar a shekara ta dubu daya da dari tara da saba'in da bakwai wato 1977 don ci gaba da karatun sakandare a makarantar sakandare ta Saint Augustine, Urua Inyang (1977-1982). Daga baya ya ci gaba da karatun shari'a a Jami'ar Calabar (1987-1991) kafin ya kammala karatun a Makarantar Shari'a ta Najeriya, Victoria Island, Legas (1991-1992). [4]
A watan Disamba na shekara ta dubu biyu da goma sha hudu wato 2014, gwamnan da ke aiki na Jihar Akwa Ibom, wato Cif Godswill Akpabio ya tura sunan Nwoko zuwa Majalisar Dokokin Jihar Akwana Ibom domin tantancewa da kuma nadin a matsayin Babban Lauyan jihar da Kwamishinan Shari'a.[5]
A ranar sha uku ga watan Janairun shekara ta dubu biyu da goma sha biyar wato 2015, an ba shi aikin. Ya zama Babban Lauyan 14 da Kwamishinan Shari'a na Jihar Akwa Ibom .
A tsakiyar shekara ta shekara ta dubu biyu da goma sha biyar wato 2015, gwamnan da ke kan mulki, Gwamna Udom Gabriel Emmanuel ya sake nada shi Babban Lauyan jihar da Kwamishinan Shari'a.[6][7][8][9][10][11]
Bayanan da aka ambata
gyara sashe- ↑ YOUR-NAME. "CELEBRATING LEGAL LUMINARY, Uwemedimo Nwoko AT 53". www.akwaibomnews.com.ng.
- ↑ "Attorney-Generals of Nigeria". 22 July 2017. Archived from the original on 12 August 2021. Retrieved 2 September 2024.
- ↑ "Akwa Ibom State Gov. Udom Emmanuel Appoints New Commissioners and Special Advisers – See Full List + Portfolios". Hypestation. 7 July 2015. Archived from the original on 23 March 2017. Retrieved 2 September 2024.
- ↑ 4.0 4.1 "Barr. Uwemedimo Nwoko". Archived from the original on 2020-09-29. Retrieved 2024-09-02.
- ↑ Theinknewspaper (23 December 2014). "Welcome to the Official Blog of THE INK Newspaper- Uyo, Akwa Ibom State.: Akpabio forwards Nwoko's name to AKHA for clearance".
- ↑ Enietan-Matthews, Timothy (18 June 2015). "Akwa Ibom Governor nominates 15 former Akpabio appointees as Commissioners".
- ↑ "Emmanuel swears-in 18 commissioners, 2 Special Advisers – Vanguard News Nigeria". 7 July 2015.
- ↑ "Akwa Ibom State Gov. Udom Emmanuel Appoints New Commissioners and Special Advisers – See Full List + Portfolios". 7 July 2015. Archived from the original on 23 March 2017. Retrieved 2 September 2024.
- ↑ "See the List of New Commissioners Appointed by Akwa Ibom State Governor, Udom Emmanuel – download music + video lyrics & song audio". 25 November 2016. Archived from the original on 10 April 2019. Retrieved 2 September 2024.
- ↑ Tori.ng; Tori.ng (25 November 2016). "See the List of New Commissioners Appointed by Akwa Ibom State Governor, Udom Emmanuel". Tori.ng.
- ↑ admin (1 March 2015). "There'll be another confab – Nwoko".