Rabi,atu sufyan Ahmad

Malama ce a cikin garin Kaduna wacce ta shahara a fannin wa'azi da da'awah acikin jihar.

farkon rayuwa

gyara sashe

An haifi Rabi acikin garin kura , ƙaramar hukuma Dake jihar Kano , Amma tayi rayuwarta ne kaf a jahar kaduna[1]

Tayi karatun firamare a cikin garin Kano ,da ta fara sakandiri seta dawo ta cigaba a garin Kaduna a wata makaranta Mai suna salamatu institute of Islamic studies Dake unguwan mu,azu a jihar kaduna.bayan ta gama seta tafi kwalejin horar da malamai Dake kaduna, daga Nan seta wuce jami,ar Ahmadu bello university a cikin garin zariya inda ta Sami digiri a fannin larabci da turanci.

sana'a da aiki

gyara sashe

Malama Rabi tun tana yarinya, ta tashi gidansu ana karatu irin na allo shi tayi itama ,ta fara tun tana yar shekara bakwai Kuma a hakan ake sakasu su koyar da wasu, sana'arta shine koyarwa Kuma ta fara tun tana yar karama.sannan Kuma tana aiki a Karamar hukumar igabin jihar Kaduna a matsayin Mai kula da harkokin ilimi.[2]

Malama Rabi tayi aikin da,awah da karatun ta duk tanada aure , sannan da gudummawar maigidanta shi ya karfafa ta a harkan da,awah, shine Kuma sila, hira da Akai da ita a BBC HAUSA, malamar tace maigidanta ne silar fadawarta harkan da,awah[3] duk wata gwagwarmaya da tayi tayi shine da aure akanta

Malama Rabi ta kasance Malama ce datai gwagwarmaya ta shiga lungu da Sako na nijeriya tai wa'azi , ta musuluntar da mutane da dama a wasu kauyuka acikin jihar Kaduna da niger da wasu sassan, Malama tayi shekara goma Sha biyu tana a kungiyar FOMWAN, sannan itace shugabar, ta kuma kasance shugaban da,awah da wasu kungiyoyin,daga baya Kuma ta kafa ta ta kungiyar Mai zaman kanta Mai suna initiative for Muslim women of Nigeria (IMWON) kungiya ce Dake taimako mata musulmai da marayu da zawarawa a addinin musulunci, inda kungiyar ta shiga lungu da sako na kasar gaba daya, harta haura kasar nijar, Malama Rabi tana daga cikin manyan malamai mata da suka yiwa addini hidima a tsawon rayuwar su.

Rasuwarta

gyara sashe

a[4]malama Rabi ta rasu ne ranar asabar a hanyar ta ta zuwa Adamawa gasan karatun musabaka na alqurani tare da daya daga cikin membobin kungiyar ta malm Aisha gumbi,sun rasu gaba dayanmu ta hanyar hadarin mota a saminaka hanyar su ta zuwa Adamawa[5][5] [6][7][8]

Manazarta

gyara sashe
  1. https://aminiya.ng/maigidana-ne-silar-yin-daawata-hajiya-rabiat-sufyan-ahmad/
  2. https://aminiya.ng/maigidana-ne-silar-yin-daawata-hajiya-rabiat-sufyan-ahmad/
  3. https://aminiya.ng/maigidana-ne-silar-yin-daawata-hajiya-rabiat-sufyan-ahmad/
  4. https://aminiya.ng/maigidana-ne-silar-yin-daawata-hajiya-rabiat-sufyan-ahmad/
  5. 5.0 5.1 https://manhaja.blueprint.ng/allah-ya-yi-wa-hajiya-rabiatu-safiyanu-ahmad-rasuwa/
  6. https://manhaja.blueprint.ng/allah-ya-yi-wa-hajiya-rabiatu-safiyanu-ahmad-rasuwa/
  7. https://manhaja.blueprint.ng/allah-ya-yi-wa-hajiya-rabiatu-safiyanu-ahmad-rasuwa/
  8. https://manhaja.blueprint.ng/allah-ya-yi-wa-hajiya-rabiatu-safiyanu-ahmad-rasuwa/