Tosin Igho
Tosin Igho furodusa ne kuma daraktan fina-finai na Najeriya.
Tosin Igho | |
---|---|
Rayuwa | |
ƙasa | Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | darakta, editan fim, Mai daukar hotor shirin fim da marubin wasannin kwaykwayo |
IMDb | nm10114820 |
Rayuwa da aiki
gyara sasheTosin shi ɗan tsohon sojan NTA ne Peter Igho.[1] Ya sami digiri na farko a fannin Visual Effects daga babbar jami'ar AFDA a Cape Town, Afirka ta Kudu, kuma ya sami wani digirin na farko a fannin ɗaukar hoto.[2][3] Ya fara aikinsa a matsayin mawaƙi sannan ya ba da umarni na bidiyon kiɗa. Ya ba da umarni na bidiyon kiɗa ga shahararrun mawaƙa kamar Mo' Hits Records, D'banj, Terry G, Faze, Yung L, Aramide da Sammie Okposo.[4]
Fina-finai
gyara sasheShi babban mai shiryawa ne tare da shirya shirye-shiryen talbijin da suka haɗa da; Once Upon A Time, Judging Matters, Love Come Back, I am Laycon.[2][1]
Shi ne darektan fim ɗin Seven2019 kuma yana aiki akan shirin Suspicious (fim da aka tsara fitar dashi a shekarar 2023).
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 "Nollywood director, Tosin Igho set to launch films showcasing Nigeria". Vanguard News (in Turanci). 2021-11-22. Retrieved 2022-07-20.
- ↑ 2.0 2.1 "Here is why Tosin Igho is currently one of the leading movie directors in Africa". Vanguard News (in Turanci). 2020-12-18. Retrieved 2022-07-20.
- ↑ "Meet Nollywood leading movie director, Tosin Igho, flying Africa". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News (in Turanci). 2020-12-16. Archived from the original on 2022-08-13. Retrieved 2022-07-20.
- ↑ ogunlami, yinka (2018-04-11). "This might be the most colourful Nollywood film you'll see in 2018". Pulse Nigeria (in Turanci). Retrieved 2022-07-20.