Tola Kasali shine tsohon Kwamishinan Ibeju-Lekki kuma Kwamishina sau biyu a jihar Legas.[1] Memba ne na Action Congress of Nigeria (ACN) wanda a yanzu ake kira da All Progressive Congress (APC). Kasali yazo a hukuma a lokacin tinubu na biyu 2003 a matsayin Kwamishinan Raya Karkara. yana gida a ma'aikata har saida lokaci na biyu da uban gidansa ya tafi da shi wani sananniyar tafiya, Hukumar Lafiya. Ya ajiye sannan ya nemi tikitin takarar gwamna Action Congress (AC), wanda gwamna mai ci yaci zaɓe. Daga ajiye aikinsa na ƙarshe a matsayin darakta janar na BRF (Babatunde Raji Fashola) ƙungiyar kamfen, Kasali ya jagoranci ma'aikatar aiki na musamman a matsayin Kwamishina.

Tola Kasali
Rayuwa
Haihuwa Lekki (en) Fassara, 7 Nuwamba, 1950 (73 shekaru)
ƙasa Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Action Congress of Nigeria (en) Fassara

Ya tsaya takarar gwamnan jihar Legas a 2007 da 2015 a karkashin jam’iyyar APC (All Progressive Congress) amma ya sha kaye a zaben fidda gwani.

A yanzu haka mamba ne a hukumar saka hannun jari ta Odua mai kula da jihohin Yamma da yake wakiltar jihar Legas.

Rayuwar farko da ilimi gyara sashe

An haifi Tola Kasali ga shahararren dangin Kasali na karamar hukumar Ibeju-Lekki; Ya taso ne a tsohuwar sashin Epe dake jihar Legas . Ya kasance likita daga Cibiyar Kiwon Lafiya ta Jiha ta Zaporozhye, Jamhuriyar Ukrainian, a cikin tsohuwar Tarayyar Soviet Socialist Republic (USSR) kuma ɗan siyasa mai tushe daga al'ummar Ibeju/Lekki na bakin teku.

Sana'ar siyasa gyara sashe

Kasali ya fara gudanar da mulki ne a lokacin da aka zabe shi a matsayin shugaban karamar hukumar ibeju-lekki. A matsayinsa na shugaba ya fara shirin karfafawa a karamar hukumar, ya kuma karfafa rabon tallafin kudi ga ‘yan asalin karamar hukumar, ya himmatu wajen inganta rayuwar al’ummar mazabarsa. Bayan wa’adinsa bola tinubu ya nada shi kwamishina har zuwa 2006.”[2]

Daga baya Gwamna Fashola ya sake nada Kasali domin ya yi aiki tare da shi, inda ya rike har zuwa shekarar 2011.[3]

Manazarta gyara sashe

Hanyoyin haɗi na waje gyara sashe