Titin Umaru Musa Yar'Adua
Titin Umaru Musa Yar’adua wanda aka fi sani da titin filin jirgin sama hanya ce mai guda 10, wadda aka sake gina ta domin magance cunkoson ababen hawa da gwamnatin Marigayi Umaru Musa ‘Yar’aduwa ke yi a kan titin kafin rasuwarsa.[1]
Titin Umaru Musa Yar'adua | ||||
---|---|---|---|---|
road (en) | ||||
Bayanai | ||||
Farawa | 1975 | |||
Ƙasa | Najeriya | |||
Lokacin farawa | 2014 | |||
Wuri | ||||
|
Titin na a matsayin babbar hanya zuwa tsakiyar birnin Abuja daga sassan kudancin ƙasar. Babban titin filin jirgin saman ya haɗe da hanyar filin jirgin Nnamdi Azikiwe zuwa tsakiyar birnin tarayya Abuja.
Sake ginawa
gyara sasheYawan zirga-zirgar ababen hawa a titin filin jirgin ne ya sa aka yi gyara tare da sake gina titin filin jirgin (wanda aka canja masa suna zuwa Umaru Yar’adua Expressway) – 37.5 kilometres (23.3 mi) a tsayi. Faɗaɗa hanyar da ake da ita zuwa tashar jirgin sama daga hanyoyi biyu zuwa uku da kuma gina sabuwar hanyar mota mai hannu biyu (na zuwa da dawowa) a kowane ɓangare.[1] An bayar da wannan aikin a kan tsabar kuɗi sama da dala biliyan 1.7 ga kamfanin gine-gine na Julius Berger.[2][3]
Marigayi Shugaba Umaru Musa 'Yar'Adua ne ya ƙaddamar da fara aikin shimfiɗa aikin a shekarar 2009 kuma a shekarar 2014 ne aka kammala. Sabbin manyan hanyoyin mota guda 10 sun ƙunshi fitulun titi, magudanun ruwa, gadoji da gadar sama, tudu, bututun sadarwa da (interchanges) da dai sauransu.
Ƙaddamarwa
gyara sasheA ranar 7 ga watan Mayun 2015, tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ne ya ƙaddamar da titin.[4][1]
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 1.2 "N59bn Abuja Airport Expressway Becoming A Death Trap". P.M. News (in Turanci). Retrieved 13 January 2022.
- ↑ "Nigeria's $1.7bn Airport Express Way Breaks Ground". RoadTraffic-Technology.com. Archived from the original on 25 December 2022. Retrieved 13 January 2022.
- ↑ Femi, Ipaye (25 August 2014). "The N257 billion ($1.7bn) Abuja Airport/Kubwa Expressway And Its Killer Open Drainage". Sahara Reporters. Retrieved 13 January 2022.
- ↑ "Umaru Musa Yaradua Expressway". Channels Television. Retrieved 13 January 2022.