Tijjani Yahaya Kaura
Tijjani Yahaya Kaura Ya kasance Dan Najeriya ne, dan siyasa wanda ya taɓa zama ƙaramin ministan Harkokin Waje na Najeriya da kuma Sakataren Gwamnati na Jahar Zamfaran, Najeriya. A yanzu shi ne Sanata mai wakiltar yankin Zamfara ta arewa a majalisar Tarayyar Najeriya. An zabe shi senata a shekarar 2015 sannan kuma aka sake zaɓen sa a karo na biyu a ranar 23 ga watan February, lokacin babban zaɓen shekara ta 2019 a Najeriya ƙarƙashin jam'iya mai mulki All Progressives Congress (APC). Shi ne ke riƙe da chairman senate committee on federal character and intergovernmental affairs.[1][2][3][4]
Tijjani Yahaya Kaura | |||
---|---|---|---|
ga Yuni, 2015 - ga Yuni, 2019 ← Sahabi Alhaji Yaú - Sahabi Alhaji Yaú → District: Zamfara North | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Kaura-Namoda, 1959 (64/65 shekaru) | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa | ||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa | All Progressives Congress |
Farkon Rayuwa
gyara sasheAn haife shi a Najeriya, a (arewacin) Zamfarar Najeriya a ranar 3 ga watan Fabrairu, shekara ta alif dari tara da hamsin da tara 1959. Shi haifaffan karamar hukumar Kauran-Namoda ne da ke a jahar ta Zamfara[5].
Siyasa
gyara sasheTijjani Yahaya Kaura kwararren dan siyasa ne a Najeriya wanda a halin yanzu sanata ne me wakiltan arewacin Zamfara kuma ya riqe matsayin SSG a baya[5].
Manazarta
gyara sashe- ↑ "APC wins Senate, Reps seats in Zamfara". www.pulse.ng (in Turanci). 2019-02-26.
- ↑ africaprimenewsblog, Author (2017-03-24). "It's Time To Reboot Nigeria-Senator Kaura". Africa Prime News (in Turanci).
- ↑ "APC wins Senate majority with 63 Senators, PDP behind with 37". www.pulse.ng (in Turanci). 2019-03-12.
- ↑ Simire, Michael (2018-01-19). "NEITI's interventions saved extractive sector from collapse, says senator". EnviroNews Nigeria - (in Turanci).
- ↑ 5.0 5.1 https://blerf.org/index.php/biography/kaura-senator-tijjani-yahaya/