The Innocent (1986 fim)
The Innocent (Larabci البرئ, lafazin: Alparee') Fim ne na kasar Masar, wanda aka saki a ranar 15 ga Agusta 1986, tare da Ƴan wasa irin su Ahmed Zaki, Gamil Ratib, da Mahmoud Abdel Aziz.
The Innocent (1986 fim) | |
---|---|
Asali | |
Lokacin bugawa | 1986 |
Asalin suna | البرئ |
Asalin harshe | Larabci |
Ƙasar asali | Misra |
Characteristics | |
Genre (en) | drama film (en) |
During | 159 Dakika |
Launi | color (en) |
Direction and screenplay | |
Darekta | Atef El Tayeb |
Marubin wasannin kwaykwayo | Wahid Hamed |
'yan wasa | |
Other works | |
Mai rubuta kiɗa | Ammar El Sherei (en) |
External links | |
Specialized websites
|
Labari
gyara sasheFim ɗin ya nuna Ahmed Sabe' El Leil (Ahmed Zaki), matashin matalauci manomi, wanda ke cika shekarar soja ta tilas. Sakamakon kwazonsa, an zabe shi a matsayin mai gadin gidan yari. A gidan yari yakan ci karo da fursunonin siyasa da ake wulakanta su. Yana bin umarnin azabtarwa da wulakanta fursunonin, har ma da aiwatar da hukuncin kisa, an kawo motocin da ke cike da daliban jami’a da suka yi rikicin biredi a shekarar 1977 zuwa wannan gidan yari, daga cikinsu akwai tsohon abokinsa Hussein Wahdan. Ta hanyar Hussein matashin mai gadi ya gano yadda ake zalunci da cin hanci da rashawa, kuma Ahmed ya ki azabtar da Hussein.[1] A fage na ƙarrshe, wanda aka yi wa katsalandan a Masar, Ahmed ya bude wuta ga jami'ai da sauran sojoji, har sai da aka harbe shi a yayin da wata sabuwar motar da ke cike da daliban tarzoma ta zo.[2]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Al Bary' (1986) The Innocent". El Cinema. Archived from the original on 2 January 2019. Retrieved 1 January 2019.
- ↑ Zeinab Abul-Magd (April 7, 2010). "Ahmed Zaki: The rise and fall of a generation". Egypt Independent. Retrieved 1 January 2019.