Austin Thabani Dube(an haife shi ranar 16 ga watan Nuwamba 1992) ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na Afirka ta Kudu wanda ke taka leda a matsayin mai tsaron baya ga kulob ɗin Afirka ta Kudu Richards Bay . An buga wa tawagar kwallon kafar Afirka ta Kudu [1]

Thabani Dube
Rayuwa
Haihuwa Cape Town, 16 Nuwamba, 1992 (32 shekaru)
ƙasa Afirka ta kudu
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
 

Aikin kulob

gyara sashe

Dube ya buga wasa a Witbank Spurs FC kafin ya koma kungiyar PSL dake Mpumalanga TS Galaxy FC Austin Dube ya koma kungiyar kwallon kafa ta Afirka ta Kudu Richards Bay FC a kakar wasa ta 2020/21 a gasar National First Division inda ya buga wasanni 6 kuma ya ci kwallo 1.

A kan 20 Yuli 2021, Dube ya sanya hannu kan kwangilar shekaru uku tare da Kaizer Chiefs . [2]

Ayyukan kasa da kasa

gyara sashe

Ya fara buga wasansa na farko a kungiyar kwallon kafa ta Afirka ta Kudu a ranar 6 ga Yuli 2021 a wasan cin kofin COSAFA na 2021 da Botswana . [3] Afirka ta Kudu ce ta lashe gasar.

Manazarta

gyara sashe
  1. "Kaizer Chiefs sign Thabani Austin Dube from Richards Bay United". SowetanLIVE (in Turanci). Retrieved 2021-07-20.
  2. "Kaizer Chiefs confirm contract details of newest Naturena signing!". thesouthafrican.com. Retrieved 20 July 2021.
  3. "South Africa v Botswana game report". ESPN. 6 July 2021. Retrieved 12 August 2021.