Taron sauyin yanayi na Majalisar Ɗinkin Duniya na 1998

An gudanar da taron sauyin yanayi na Majalisar Ɗinkin Duniya na 1998, a watan Nuwamba 1998 a Buenos Aires, Argentina.[1] Taron ya haɗada taron kasashe karo na 4 (COP4) ga tsarin Majalisar Ɗinkin Duniya kan sauyin yanayi (UNFCCC). An yi tsammanin za'a kammala sauran batutuwan da ba'a warware su ba a Kyoto a wannan taron. Duk da haka, rikitarwa da wahalar samun yarjejeniya a kan waɗannan batutuwa sun kasance ba za a iya warwarewa ba, kuma a maimakon haka ɓangarorin sun amince da "Shirin Aiki" na shekaru 2 don cigaba da ƙoƙari da kuma tsara hanyoyin aiwatar da yarjejeniyar Kyoto, wanda za'a kammala nan da shekara ta 2000. A yayin taron, kasashen Argentina da Kazakhstan sun bayyana aniyarsu ta daukar nauyin rage fitar da hayaki mai gurbata muhalli, ƙasashe biyu na farko da ba na Annex ba.

Taron sauyin yanayi na Majalisar Ɗinkin Duniya na 1998
United Nations Climate Change conference (en) Fassara
Bayanai
Ƙasa Argentina
Mabiyi 1997 United Nations Climate Change Conference (en) Fassara
Ta biyo baya 1999 United Nations Climate Change Conference (en) Fassara
Kwanan wata 2 Nuwamba, 1998
Lokacin farawa 2 Nuwamba, 1998
Lokacin gamawa 14 Nuwamba, 1998
Shafin yanar gizo unfccc.int…
Wuri
Map
 34°34′57″S 58°23′23″W / 34.5824°S 58.3897°W / -34.5824; -58.3897

Manazarta

gyara sashe
  1. "4th Conference of the Parties to the UNFCCC: United Nations Framework Convention on Climate Change, 2nd to 13th November 1998, Buenos Aires, Argentina: Greenhouse Gas Emissions-Graphics | GRID-Arendal". www.grida.no. Retrieved 2023-09-24.