Sudan TV
Sudan TV ko Sudan National Broadcasting Corporation (SNBC) cibiyar sadarwar talabijin ce ta harshen Larabci. Cibiyar sadarwar ƙasar Sudan ce kuma mallakar gwamnati ce kuma gwamnatin ce ke sarrafa ta. Sudan TV na ɗaya daga cikin gidajen talabijin guda shida a ƙasar.[1]
Sudan TV | |
---|---|
Bayanai | |
Iri | tashar talabijin |
Ƙasa | Sudan |
Mulki | |
Mamallaki | Government of Sudan (en) |
Tarihi | |
Ƙirƙira | 1962 |
|
Tarihi
gyara sasheA shekarar alif dari tara da sittin da biyu 1962, gidan talabijin na Sudan ya fara watsa shirye-shirye a yankin babban birnin ƙasar wato Khartoum. Ana iya samun siginar a gundumomi uku da suka haɗa da ; babban birnin Khartoum, Omdurman da Khartoum Bahri . Bayan shekara guda, Janar Mohmaed Talat Fareed ya kafa tashar a matsayin mai watsa shirye-shiryen watsa shirye-shirye na ƙasa kuma ya sanya hannu kan kwangila tare da mai watsa shirye-shiryen watsa shirye-shirye na Yammacin-Jamus-(West-German) don ba da tallafin fasaha, kyamarori da na'ura.
A cikin shekarun alif dari tara da 1970, gidan talabijin na Sudan ya faɗaɗa watsa shirye-shiryensa, lokacin da Babban Kamfanin Sadarwa (Wireless and Wired Telecommunications) ya gina tashar tauraron dan adam. A cikin shekara ta alif dari tara da saba'in da shida1976, gidan talabijin na Sudan ya fara watsa shirye-shiryen sa a cikin launi madadin na rashin kala, baki da fari.
Shirye-shirye
gyara sasheShirye-shiryen gidan telebijin ɗin sun haɗa da labarai, addu'o'i, karatun kur'ani da nishadantarwa iri-iri, kamar shirye-shiryen yara, gasa masu basira, wasan kwaikwayo da sauran shirye-shirye.[2] Wani soji yana aiki tare da gidan talabijin na Sudan don tabbatar da cewa shirye-shiryen sun yi dai-dai da manufofin gwamnatin ƙasar.[1]
Tashoshi
gyara sasheSudan TV tana watsa shirye-shirye a tashoshi ƙwara biyu, kuma ana samun su ta tauraron dan adam.[1]
Duba kuma
gyara sashe- Sadarwa a Sudan
- Media na Sudan
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 1.2 "Sudan profile - Media". BBC News (in Turanci). 2011-07-09. Retrieved 2023-02-21.
- ↑ www.sudantv.net https://web.archive.org/web/20110712174055/http://www.sudantv.net/. Archived from the original on 2011-07-12. Retrieved 2023-02-21. Missing or empty
|title=
(help)