Steven Folly Nador (an haife shi a ranar 23 ga watan Yuni 2002) ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne wanda ke taka leda a matsayin ɗan wasa mai tsaron baya ga ƙungiyar Serie C ta Italiya Montevarchi Aquila a matsayin aro daga kulob ɗin SPAL. An haife shi a Jamus, yana wakiltar Togo a duniya.

Steven Nador
Rayuwa
Haihuwa Krefeld, 23 ga Yuni, 2002 (21 shekaru)
ƙasa Jamus
Togo
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
 

Aikin kulob gyara sashe

Bayan fatarar kulob dinsa na Chievo, a watan Agusta 2021 Nador ya koma tawagar 'yan kasa da shekaru 19 na SPAL.[1]

Ya buga wasansa na farko a Seria B a SPAL a ranar 6 ga watan Nuwamba 2021 a wasan da suka yi da Cremonese. [2]

A ranar 1 ga watan Satumba 2022, Montevarchi Aquila ta ba Nador aro. [3]

Ayyukan kasa da kasa gyara sashe

A ranar 18 ga watan Maris 2022, an kira Nador zuwa tawagar kasar Togo .[4] Ya yi wasan sa na farko tare da su a matsayin ɗan canji a wasan sada zumunci da suka yi rashin nasara da ci 2-1 a Ivory Coast a ranar 25 ga watan Satumba 2022.[5]

Rayuwa ta sirri gyara sashe

An haife shi a Jamus, ya girma a Faransa kuma dan asalin Togo ne. [6]

Manazarta gyara sashe

  1. "PRIMAVERA – I NUOVI ARRIVI DELLA FORMAZIONE BIANCAZZURRA" (in Italian). SPAL . 12 August 2021. Retrieved 26 November 2021.
  2. "Cremonese v SPAL game report" . Soccerway. 6 November 2021.
  3. "Il difensore classe 2002 approda a Montevarchi dalla SPAL" (in Italian). Montevarchi Aquila. 1 September 2022. Retrieved 16 September 2022.
  4. "Éperviers : Ouro-Gneni et Ouro-Agoro forfaits" (in French). Togolese Football Federation . 18 March 2022. Retrieved 20 March 2022.
  5. "%competition_name% (Sky Sports)" . Sky Sports .
  6. "NEXT GEN – STEVEN NADOR" (in Italian). SPAL . 10 March 2022. Retrieved 20 March 2022.

Hanyoyin haɗi na waje gyara sashe