Steevan Humberto Fortes dos Santos (an haife shi a ranar 17 ga watan Satumba 1989), wanda kuma aka fi sani da "Duba", ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na Cape Verde wanda ke taka leda a matsayin ɗan wasan gaba ga kungiyar Union Omaha ta USL League One.

Steevan Dos Santos
Rayuwa
Haihuwa Mindelo (en) Fassara, 17 Satumba 1989 (34 shekaru)
ƙasa Cabo Verde
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
  Pittsburgh Riverhounds SC (en) Fassara-
CS Mindelense (en) Fassara2007-2012
Ullensaker/Kisa IL (en) Fassara2012-20144921
  Cape Verde national football team (en) Fassara2013-10
Progresso Associação do Sambizanga (en) Fassara2014-2015
  Rochester New York FC (en) Fassara2015-
 
Muƙami ko ƙwarewa Ataka
Lamban wasa 10
Nauyi 87 kg
Tsayi 195 cm

Sana'a gyara sashe

Duba ya fara aikinsa a ƙasarsa ta Cape Verde a kulob ɗin CS Mindelense, kafin ya koma Norway a ƙungiyar Ullensaker/Kisa IL a 2012.[1] Bayan ɗan gajeren lokaci a kulob ɗin Progresso na Angola, Duba ya sanya hannu tare da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta United Soccer League Rochester Rhinos a ranar 27 ga watan Maris 2015.[2]

Bayan kaka biyu tare da kulob ɗin Ottawa Fury FC, Duba ya koma Pittsburgh Riverhounds SC a ranar 8 ga watan Janairu 2019 akan yarjejeniyar shekara guda. [3]

A ranar 24 ga watan Disamba, 2020, an sanar da cewa Duba zai shiga ƙungiyar USL Championship ta Tampa Bay Rowdies gabanin kakarsu ta 2021. [4] Tampa ta sake shi bayan kakar 2022.[5]

Dos Santos ya rattaba hannu tare da Union Omaha a ranar 7 ga watan Fabrairu, 2023. [6]

Manazarta gyara sashe

  1. "Looking at 9 Players on Trial with the Rhinos" . The Bent Musket . Retrieved 2017-07-19.
  2. "News" . www.rhinossoccer.com . Retrieved 2017-07-19.
  3. Staff, Riverhounds (8 January 2019). "Hounds sign forward Steevan Dos Santos" . Pittsburgh Riverhounds SC - USL.
  4. "Rowdies Sign Forward Steeven Dos Santos" .
  5. USLChampionship com Staff (December 2, 2022). "Tampa Bay Rowdies announce initial 2023 roster decisions" . USL Championship .
  6. USLChampionship com Staff (February 7, 2023). "UNION OMAHA SIGNS FORMER TAMPA BAY ROWDIES FORWARD STEEVAN DOS SANTOS" . unionomaha.com .