Obotuke Timothy Ochuko Sirbalo, wanda aka fi sani da Sirbalo ko Sirbalo Clinic (an haife shi a ranar 27 ga watan Maris, shekara ta alif 1992). ɗan wasan kwaikwayo ne na Najeriya, ɗan wasan barkwanci kuma marubuci.[1][2][3]

Sirbalo
Rayuwa
Haihuwa Delta, 27 ga Maris, 1992 (32 shekaru)
ƙasa Najeriya
Sana'a
Sana'a Jarumi
hoton sirbalo

Tarihin Rayuwa gyara sashe

An haifi Sirbalo a garin Warri da ke jihar Delta a Najeriya.Ya yi karatu a kwalejin gwamnatin tarayya Idoani da jami'ar jihar Legas.[4]

Sirbalo ya fara edita a Nollywood a shekarar 2014. Har ila yau, ya kasance darakta na sarrafin musamman.

Sirbalo ya shiga wasan barkwanci a shekarar 2016 a matsayin edita kuma darakta. Aikin wasan kwaikwayonsa ya fara ne a cikin 2017. An fi saninsa da zama tauraro a fina-finan nasara na Nollywood box-office kamar Okafor's Law (2017),  Bling Lagosians (2019).

Yana da tashoshin YouTube 5 da masu biyan kuɗi miliyan 1. Yana da mabiyan Fezbuk miliyan 7.5.

An fi saninsa da "Sirbalo and bae" da " Mallen college”.[5]

Sirbalo a halin yanzu yana daya daga cikin hamshakan attajiran barkwanci a Najeriya.[6]

Fina-finai gyara sashe

  • My Village People, 2021
  • Bling Lagosians, 2019
  • 10 Days in Sun City, 2017
  • Okafor's Law, 2017

Hanyoyin haɗi gyara sashe

Manazarta gyara sashe

  1. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2021-10-22. Retrieved 2021-10-22.
  2. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2021-10-22. Retrieved 2021-10-22.
  3. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2021-10-22. Retrieved 2021-10-22.
  4. https://www.thefamousnaija.com/2020/10/timothy-obotuke-sirbalo-biography-age.html
  5. https://www.tuko.co.ke/398835-kenyan-actress-naava-queen-appearance-popular-sirbalo-comedy-show.html
  6. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2021-10-22. Retrieved 2021-10-22.