Shivakiar Ibrahim
Shivakiar Ibrahim (A 25 ga watan Oktoba shekara ta 1876 zuwa 17 ga watan Fabrairu shekara ta 1947 [ kuma Gimbiya ce ta kasar Masar kuma memba ce a Daular Muhammad Ali. Ita ce matar farko ta Sarki Fuad I.
Shivakiar Ibrahim | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Üsküdar (en) , 25 Oktoba 1876 |
Mutuwa | Kairo, 17 ga Faburairu, 1947 |
Makwanci | Tomb of Princess Shawikar (en) |
Ƴan uwa | |
Abokiyar zama | Fuad I of Egypt (en) |
Yara |
view
|
Yare | Muhammad Ali dynasty (en) |
Sana'a |
Wannan mukalar bata da Reference (Manazarta) ko daya, ka taimaka ta hanyar samar da Manazarta daga littafi ko yanar gizo, duba wannan shafin domin samun masaniya akan yanda zaka samar da Reference (Manazarta) a cikin wannan mukalar.
. |
Rayuwa ta farko
gyara sasheAn haifi Gimbiya Shivakiar Ibrahim a ranar 25 ga watan Oktoba shekara ta 1876 a Üsküdar (tsohon Scutari), Istanbul . Ita ce kawai 'yar Yarima Ibrahim Fahmi Pasha (a shekara ta 1847 zuwa shekara ta 1893), da matarsa ta farko, Nevjiwan Hanim a (shekara ta 1857 zuwa shekara ta 1940). Ita ce jikokin Yarima Ahmad Rifaat Pasha a (shekara ta 1825 zuwa 1858) da Shams Hanim (ya mutu shekara ta 1891). Shivakiar yana da 'yan'uwa biyu, Yarima Ahmad Saif ud-din Ibrahim (a shekara ta 1881 zuwa shekara ta 1937), da Yarima Muhammad Wahid ud-din Abraham. Gwaggowarta Gimbiya Ayn al-Hayat Ahmad ita ce matar farko ta Sultan Hussein Kamel .