Shirin "The Real Housewives of Lagos"
Shirin "The Real Housewives of Lagos" | |
---|---|
Asali | |
Asalin suna | The Real Housewives of Lagos |
Ƙasar asali | Najeriya |
Characteristics | |
Genre (en) | reality television (en) |
'yan wasa | |
The Real Housewives of Lagos (wanda aka rage wa RHOLagos ) jerin shirin talabijin ne na gaskiya na Najeriya wanda aka fara a ranar 8 ga watan Afrilun 2022, a tashar Showmax, tare da 'yan wasa kaman Carolyna Hutchings, Laura Ikeji, Chioma Ikokwu, Toyin Lawani-Adebayo, Iyabo Ojo, da Mariam Timmer.[1] Shirin ya mayar da hankali ne kan rayuwar ƙawa a Legas, tun daga shagunan sayayya, shagulgula, tafiye-tafiye, da gasa tsakanin ƙungiyoyin zamantakewa.
Matan gidan asali na Legas wani shiri ne daga jerin fina-finan Faransa "The Real Housewives" wanda kuma Livespot 360 suka shirya.[2]
Dubawa & jefa
gyara sasheMatan gida | Lokaci | |
---|---|---|
1 | 2 | |
Carolyna Hutchings | Babba | |
Laura Ikeji | Babba | |
Chioma Ikokwu | Babba | |
Toyin Lawani-Adebayo | Babba | |
Iyabo Ojo | Babba | |
Mariam Timmer | Babba | |
Faith Morey | Babba | |
Tania Omotayo | Babba | |
Abokan matan gida | ||
Priscilla Ajoke Ojo | Aaboki | |
Paul O | Aaboki | |
Vanessa Onyinye | Aaboki | |
Rommel Asagwara | Aaboki |
Carolyna Hutchings ita ce Shugabar wani kamfani, noma, mai da iskar gas, kuma uwa ga 'ya'ya uku.
Laura Ikeji
gyara sasheLaura Ikeji-Kanu mai jawo hankali ce a kafafen sada zumunta, marubuci, kuma ƴar kasuwa. Ita uwa ce da yara biyu, kuma ta auri Christopher Kanu.
Chioma Ikoku
gyara sasheChioma Ikokwu lauya ce, wacce suka kafa kuma Shugaba na kamfanin gyaran gashi "Good Hair Woman and Brass", da Gidan Abinci na Copper & Lounge. Haka kuma tana gudanar da ayyukan agaji na mata da yara mai suna Goodway Foundation.
Toyin Lawani-Adebayo
gyara sasheToyin Lawani-Adebayo mashahuriyar masaniyar kwalliya ce, mai zanen kaya, hamshakiyar 'yar kasuwa kuma Shugaba na Tiannah's Place Empire. Ita ce mahaifiyar 'ya'ya uku kuma ta auri Segun Wealth.
Iyabo Ojo fitacciyar 'yar wasan kwaikwayo ce ta Nollywood, furodusa, mai tasiri, 'yar kasuwa kuma Shugaba na Fepris Limited. Bazawara ce kumauwa ga 'ya'ya biyu.
Mariam Timmer
gyara sasheMariam Timmer ƙwararriyar PR ce kuma babbar darektan gudanarwa a hukumar Six Sixteen Agency.
Shirye-shirye
gyara sasheLokaci | Shirye-shirye | Watsawa ta asali | |
---|---|---|---|
Watsawa ta farko | Watsawa ta ƙarshe | ||
1 | 14 | Afrilu 8, 2022 | 8 ga Yuli, 2022 |
2 | 4 | Satumba 29, 2023 |
Shiryawa
gyara sasheLivespot 360 ne ya shirya jerin shirye-shiryen talabijin na gaskiya, kuma NBCUniversal Formats ya rarraba, sashin Universal Studio Group. A ranar 13 ga watan Janairun 2022, Shirin Labaran Showmax sun ba da labari game da shirin, kuma sun gabatar da 'yan wasan shirin. A ranar 16 ga Maris 2022, an fitar da tirela a hukumance akan tashar YouTube ta Showmax. A ranar 29 ga Agusta 2023, Showmax ya tabbatar da Faith Morey, da Tania Omotayo don shiga cikin manyan jarumai a kakar wasa ta biyu na Matan Gidan Gida na Legas. A ranar 7 ga Satumba 2023, Showmax ya buɗe tirelar hukuma ta kakar wasa ta biyu na jerin. A ranar 23 ga Satumba, 2023, an gudanar da wani biki mai zaman kansa a Legas gabanin fitar da kashi na biyu na shirin.