Shaleen Surtie-Richards
Shaleen Surtie-Richards an haife ta 7 Mayu na shekarar 1955 ta mutu a 7 yuni 2021[1][2]) ta kasance ƴar wasan talabijin ta Afirka ta Kudu, haka-zalika ƴar wasan fina-finai, wataƙila an fi saninta da rawar da ta taka a fim ɗin Fiela se Kind na shekarar 1988 da kuma jerin dogon gudu na Egoli: Place of Gold. Ta yi wasa a cikin harsunan Afirka da Ingilishi.
Shaleen Surtie-Richards | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Upington (en) , 7 Mayu 1955 |
ƙasa | Afirka ta kudu |
Mutuwa | 7 ga Yuni, 2021 |
Karatu | |
Harsuna | Turanci |
Sana'a | |
Sana'a | jarumi da ɗan wasan kwaikwayo |
IMDb | nm0839741 |
Rayuwa ta farko da aiki
gyara sasheAn haifi Surtie-Richards a Upington, Lardin Cape, Tarayyar Afirka ta Kudu, a ranar 7 ga watan Mayu 1955 ta halarci makaranta a can da birnin Cape Town. Mahaifinta shugaban makaranta , kuma mahaifiyarta malama ce. Ta girma a lokacin wariyar launin fata, ta bayyana cewa asalin ta ba shi da talauci. [3] A lokacin da take yarinya, lokacin da makarantar kiɗa ta gida ba za ta yarda da ita ba saboda launi, mahaifinta ya saya mata piano. [3] Ta dauki darussan ballet da tennis.
Ayyukan fim
gyara sasheSurtie-Richards ta taka rawar gani a fina-finan nan masu zuwa:[4]
- Fiela se Kind (1988)
- Mama Jack (2005)
- Egoli: Afrikaners Is Plesierig (2010)
- Knysna (2014)
- Treurgrond (2015)
- Twee Grade van Moord (2016)
- Vaselinetjie (2017)
- Slay (2021)
Mutuwa
gyara sasheSurtie-Richards ya mutu ranar 7 ga watan Yuni 2021, tana da shekaru 66 a duniya. Ta mutu da dare a cikin barcin ta kuma tana fama da matsalolin kiwon lafiya da yawa. Iyalinta sun musanta jita-jita cewa mutuwarta na da alamun sakamakon kashe kanta.
Manazarta
gyara sashe- ↑ Naidoo, Deepika; Thakurdin, Karishma (7 June 2021). "Shaleen Surtie-Richards has died". Sowetan Live (in Turanci).
- ↑ "Actress Shaleen Surtie-Richards dies". ENCA (in Turanci). Johannesburb. 7 June 2021. Archived from the original on 7 June 2021. Retrieved 5 March 2024.
- ↑ 3.0 3.1 Cite error: Invalid
<ref>
tag; no text was provided for refs namedFleurVeteran
- ↑ "Shaleen Surtie-Richards". IMDb: Internet Movie Database. Retrieved 5 December 2016.