Seyni Garba
Manjo Janar Seyni Garba (an haife shi 1 ga Janairu 1953, a Garankedey, Yankin Dosso, Niger ) janar ne na sojojin Nijar. Ya kammala karatunsa na firamare da sakandare a Dosso da kuma makarantar sakandaren Korombé da ke Yamai tsakanin 1966 da 1974, kafin ya halarci jami’ar Abdou Moumouni da ke Yamai, sashen ilimin Lissafi - Fasaha a 1974. Shi ne babban hafsan hafsoshin sojojin Nijar tun daga shekarar 2011, inda yake jagorantar yaƙi da Boko Haram . Yayi aure kuma yana da yara biyar.
Seyni Garba | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Garankédey (en) , 1 ga Janairu, 1953 (71 shekaru) |
ƙasa | Nijar |
Karatu | |
Harsuna | Faransanci |
Sana'a | |
Sana'a | hafsa da Mai wanzar da zaman lafiya |