Sauro
Sauro Yana da ƙafafu huɗu kuma yana da fuka-fukai biyu yana cikin dabbobi irin waɗanda ke tashi shima kamar kowane halittu ne yana da mace da namiji yana shan jinin mutun har yasa masa zazzaɓin ciwon Sauro[1], Sauro na ɗaya daga cikin masu yaɗa cututtukan da suka fi yin kisa a duniya, inda ta ke kama miliyoyin mutane a kowace shekara. Yara fiye da miliyan ɗaya suke mutuwa kowace shekara a sanadin wannan cuta da Sauro ke yaɗa ta. Abin tayar da hankali shi ne a yanzu an ga alamun cewa sauro ya fara jurewa magungunan kashe kwarin da ake yin amfani da su wajen kashe shi. Amma kuma a wani bincike da Ɗaliban Jami'ar Kimiyya da fasaha ta jihar Kano dake Wudil, KUST, Wanda Al'amen Baba ke jagoranta sun gano wasu kwayoyin halitta a jikin sauron waɗanda suke sanya shi jurewa Wadannan magunguna.
Sauro | |
---|---|
Scientific classification | |
Kingdom | Animalia |
Phylum | Arthropoda |
Class | insect (en) |
Order | Diptera (en) |
Superfamily | Culicoidea (en) |
dangi | Culicidae Meigen, 1818
|
Wannan mukalar bata da Reference (Manazarta) ko daya, ka taimaka ta hanyar samar da Manazarta daga littafi ko yanar gizo, duba wannan shafin domin samun masaniya akan yanda zaka samar da Reference (Manazarta) a cikin wannan mukalar.
. |
Hilary Ranson ta Makarantar nazarin Cututtukan dake Addabar Ƙasashe Masu Zafi ta ce ɗaya daga cikin muhimman makaman da ake yin amfani da su wajen hana yaɗuwar zazzaɓin cizon sauro shi ne ta yin amfani da gidan sauro. Amma kuma, tilas ne gidan sauron a ringa jiƙa shi sau da dama cikin shekara guda da wani maganin kashe kwari, musamman magunguna dangin Pyrethroid.
Ranson ta ce, "waɗannan magungunan kashe kwari sun samu nasara sosai wajen daƙile zazzaɓin cizon sauro, amma a cikin 'yan shekarun nan mun ga sauron ya fara jure ma irin waɗannan magunguna. Wannan kuwa ya dame mu sosai a saboda ba mu da wasu magungunan masu yawa da zasu iya maye gurbinsu."
Ranson ta ce akwai wasu yankuna na Afirka inda ake samun karin sauro mai ɗauke da kwayar cutar maleriya dake jure magungunan kashe kwari dangin Pyrethroid. A saboda haka ne ita da wasu masana na ƙasa da ƙasa suka nemi sanin abinda ya sa sauron ya fara jurewa magungunan.
Ta ce, "mun gano wasu ruwayen halitta guda biyu waɗanda yawansu a jikin sauro mai jurewa magungunan ya zarce yadda yake a jikin sauron da ba ya iya jurewa. Haka kuma mun samu nasarar nuna cewa waɗannan ruwayen halitta su na iya lalata magunguna kashe kwarin. Wannan shi ya sa sauron da yake ɗauke da waɗannan ruwaye biyu yana iya narkarwa ya lalata magungunan kashe kwarin da suka taɓa jikinsa, ta yadda ba zasu iya yi masa komai ba balle su kashe shi."
Haka kuma Ranson da sauran masanan sun samu nasarar gano kwayar halittar dake samar da waɗannan ruwaye a jikin sauron. Ta ce wannan abu ne mai matuƙar muhimmanci.
"A yanzu zamu iya yin sauyi ga maganin kwarin ta yadda zai iya kashe koda sauron dake da irin wadannan ruwayen. Hanyar da zamu bi mu yi haka kuwa, ita ce ta sauya sinadaran dake cikin magungunan domin canja fasalin aikinsu ta yadda a bayan kashe sauron, zasu kuma hana kwayayen halittar sauro sarrafa wadannan ruwaye. Ta yin haka, maganin zai jima sosai cikin kaifinsa a jikin kowane irin sauro. Wannan zai maido da kaifin magungunan."
Anason ta ce wannan bayanin zai taimaka⁸ wajen tabbatar da ci gaban makami mai kaifi da amfani a yakin da ake yi da zazzabin cizon sauro. An buga sakamakon wannan bincike nata a cikin mujallar nan mai suna "Genome Research".
Wurin da yake taruwa
gyara sasheSauro yana taruwa a wurin zubda ruwa har ya taru se matarsa ta shiga ciki dan tayi kwai kawa ruwa sama in ya taru ko ruwan wanka in ya taro.