Sashen Yamoussoukro
Sashen Yamoussoukro sashi ne na kasar Ivory Coast. Akwai babban birnin siyasa na Ivory Coast a karkashin sashen wato Yamoussoukro, kuma yana ɗaya daga cikin sassan biyu a gundumar Yamoussoukro mai cin gashin kanta.
Sashen Yamoussoukro | |||||
---|---|---|---|---|---|
department of Ivory Coast (en) | |||||
Bayanai | |||||
Ƙasa | Ivory Coast | ||||
Babban birni | Yamoussoukro | ||||
Wuri | |||||
| |||||
Ƴantacciyar ƙasa | Ivory Coast | ||||
District of Ivory Coast (en) | Yamoussoukro Autonomous District (en) |
Yawan jama'a da ƙananan hukumomi
gyara sasheDangane da ƙidayar shekara ta 2014, Sashen Yamoussoukro na da yawan jama'a akalla mutum 310,056. [1] An raba sashen zuwa kananan hukumomi biyu, Yamoussoukro da Kossou.
Tarihi
gyara sasheAn kafa Sashen Yamoussoukro a shekara ta 1988 azaman yanki na matakin farko yayin da aka rarraba Sashen Bouaké.[2] A shekara ta 1997, an gabatar da yankuna a matsayin sabon yanki na matakin farko na Ivory Coast; sakamakon haka, an mayar da dukkan sassan zuwa sassa na biyu. An haɗa Sashen Yamoussoukro a karkashin Yankin Lacs.
A cikin shekara ta 1998, an raba Sashen Yamoussoukro don kafa Sashen Tiébissou. [2] An sake raba Sashen Yamoussoukro a shekara ta 2009 don ƙirƙirar Sashen Attiégouakro. [2]
A cikin shekara ta 2011, an gabatar da gundumomin a matsayin sabbin yankuna a mataki na farko na kasar Ivory Coast. Bugu da kari, an sake tsara yankuna kuma sun zama yanki na biyu kuma an mayar da dukkan sassan zuwa matakai na uku. A wannan lokacin, Sashen Yamoussoukro ya zama wani yanki na gundumar Yamoussoukro mai cin gashin kansa, ɗaya daga cikin gundumomi biyu na ƙasar waɗanda ba su da yankuna.
Bayanan kula
gyara sashe- ↑ "Côte d'Ivoire", geohive.com, accessed 24 February 2016.
- ↑ 2.0 2.1 2.2 "Regions of Côte d'Ivoire (Ivory Coast)", statoids.com, accessed 16 February 2016.