Sardauna Memorial College
Sardauna Memorial College (SMC) wacce aka fi sani da suna Sheikh Sabah College, Kaduna. Makarantar sakandari ce a kaduna wanda Sarkin Kuwait Sheikh Sabah Al-Ahmad Al-Jaber Al-Sabah ya kafa a jihar Kaduna yayin ziyara, bayan rasuwar Firayim Ministan Arewacin Najeriya Sir Ahmadu Bello makarantar ta canza sunan ta zuwa Sardauna Memorial College, ga abin da yake a yau kamar yadda Sardauna Memorial College (SMC). Ana gudanar da sallar juma'a a Massalacin Wanda kungiyar izala take daukar ragamar massalacin da gudanar da da'awa da dai sauran su.
Sardauna Memorial College |
---|
Tarihi
gyara sasheCibiyar Inshorar da Ma'aikata ta Najeriya wacce ake kira (NDIC) ta ba da gudummawar miliyan N24.9 na Kwalejin Sardauna Memorial (SMC) Kaduna, don samar da e-libarary.
Alumni
gyara sasheTsofaffin daliban makarantar tana da wata kungiya da ake kira Sardauna Memorial College Old Boys Association, SAMOBA, Wadannan sunayen manyan mutane ne dasuka halarci makarantan
- Ahmad Abubakar Gumi
- Muhammadu Lawal Bello
- Jika Dauda Halliru
- Shehu Ladan
- Usman Shehu Bawa
Manazarta
gyara sasheDaliban SMC ne suka fara cin gasar kwallon kafa na makarantun sakandare na duniya a ƙasar Finland.