Sandra Aguebor ko Aguebor-Ekperuoh (an haife ta 1957) a Nijeriya, bakanikiya ce. An ruwaito cewa ita ce mace ta farko da ta fara sana'ar kanikanci a Najeriya. Ita ce kuma ta ƙirƙiro "Lady Mechanic Initiative", da ke koyar da mata marasa galihu don zama kanikawa, kuma su dogara da kansu. Da take magana kan rashin dai-dai to tsakanin maza da mata da kuma alfarmar maza, Aguebor ta bayyana cewa dole ne ta sanya himma fiye da sau biyar fiye da yadda ake daukar maza da muhimmanci, amma, ta yi tir da sanyawa abokan aikinta "Lady mechanic" maimakon "makaniki" kawai. A shekarar 2015, ta kasance batun wani fim, wanda gidan talabijin na Aljazeera ya shirya, mai taken Sandra Aguebor: The Lady Mechanic, fim din ya sami lambobin yabo a bikin Fim na New York. cikkakkiyar yar Nigeria ce Mai karajin yaqin neman byaci

Sandra Aguebor
Rayuwa
Haihuwa Birnin Kazaure, 1970 (53/54 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Pan-Atlantic University
Sana'a
Sana'a mechanical engineer (en) Fassara

Karramawa

gyara sashe

An zaɓe ta ne don lambar yabo ta COWLSO, wani shiri da gwamnatin Legas ta kafa a 1974 don karrama mutanen da suka ba da gudummawa wajen "jin dadin zamantakewar jihar". Dolapo Osinbajo da Gwamna Akinwunmi Ambode ne suka ba ta lambar yabo ta mata ta kwazo a shekara, waɗanda suka lura cewa ta yi amfani da "iyawarta da hazakarta don yin tasiri mai kyau ga al'umma a yankin da maza suka mamaye". Gwamnatin tarayyar Najeriya kuma ta ba ta lambar yabo ta ƙasa.

Da take magana da jaridar Vanguard, a wajen bikin yaye wasu mata masu kanikanci guda 50, Aguebor ya bayyana cewa ta horar da sama da kanikanci 700 zuwa yanzu. Tana da aure da yara.

Manazarta

gyara sashe