Sana'oin ƙasar Hausa
Wannan mukalar bata da Reference (Manazarta) ko daya, ka taimaka ta hanyar samar da Manazarta daga littafi ko yanar gizo, duba wannan shafin domin samun masaniya akan yanda zaka samar da Reference (Manazarta) a cikin wannan mukalar.
. |
Duk wanda kuma ya tashi ƙasar Hausa to akwai wata sana'a da ya ke yi domin dogaro dakai irin wadannan sana'o'in hausa su kanyi tasiri matuƙa a ɓangarorin al'umman HAUSAWA dama sauran ƙabilu awannan Nahiya.
Ire-iren sana'o'in Hausa
gyara sashe- Noma
- Kasuwanci
- kiwo
- Dillanci
- ƙodago
- Jima
- Dukanci
- Fawa
- Wanzamci.
Noma
gyara sashe“Noma na duke tsohon ciniki, kowa yazo duniya kai ya tarar”.. wannan shine taken Noma.
Noma sana'ace wacce ta bambanta da sana'o'in Hausawa, ba kasafai ake samun kowane al'umma acikin taba musamman mutanan birni, sai dai mutanen karkara suka fi yinta. sana'ar Noma sana'ace da ba a gadonta kowa da kowa kan iya fadawa cikin ta, kuma akwai Riba ga masu gudanar da ita, Malami da ba sarake, attajiri da talaka sukan gudanar da ita.
Ire-iren Noma
gyara sasheNoma da ya kasu kashi biyu, akwai na Noman Rani, akwai na Damina, wanda akeyi bayan Damina ta sauka, Damina takan yi a ƙalla wata biyar ko Shida, a wannan lokacin ake yin aikace aikace gona, wato yin shuka ya fito har takai damar an girbe ta, sannan akai amfanin Gida domin aci ko a sayar.
Noman Rani
gyara sasheshine akeyi yayin da Damina ta dauke, ko ayayin da ruwa ya dauke, akanyi Noma Rani a wuraren masu dausayi da ƙoramu, irin wannan noma akan yi shi ta fuskan ban Ruwa ne ga ita shukar, a wannan shi ake kira da Noman Rani kuma akwai alfanu gaya musamman mutanen da sukayi makwabtaka da Ruwa.
Noma Don ci
gyara sasheKowane manomi babban burinsa ya Noma kayan hatsi wanda kuma akalla zai kai shi har ƙarshen shekara byi awo ba, Gazawa ce ga monomi ace baya iya noma ta kai shi shekara. manomi yakan yi noman kamar su Gero
- Dawa
- Maiwa,
- Wake
- Masara
- Doya
- Dan kali... da sauransu.
Bayan manomi ya ware wadataccen abincin sa domin iyalinsa a wasu lokutan yakan ware wanda zai sayar domin takin Gona.
Noma domin sayarwa
gyara sasheManomi yakan Noma kayan sayarwa kamar su;
- Tumaturi
- Albasa
- Attarugu
- Alaiyaho
- Kabewa
- Tattasai
- Gyada
- Ridi
- Barkono
- Auduga... da sauransu.
Irin wannan noma manomi yakan yi shine ba Don yaci ba a'a sai dan ya biya buƙatar sa ko don amfanin shi ko hidima da take jiran sa na bukukuwan ƴaƴan sa.
kayan aikin Gona
gyara sashekayan aikin gona sun hada da Magirbi, da fartanya, da [[sungumi]], da gatari, da [[galma]] da [[lauje]] har dama manjagara da sauransu.
Kasuwanci
gyara sashekasuwa hanya ce ta saye da sayarwa, mai irin wannan harka shine ake kira da ɗan kasuwa idan mace ce ana mata kirari da ƴar kasuwa. kasuwanci yana wuya idan babu jari, jari shine kasuwanci, domin da jari ake cinikai ya. dole mai harkan kasuwanci sai yayi yun kurin jari da shine zai jujjuya domin ya siya kaddara yaci riba.
ire-iren kayan cinikayya
gyara sasheitadai kasuwa wuri ne da ake gudanar da saye da sayarwa, kusan kowane abin sayarwa zaka iya samu a kasuwa. kasuwa ta hada da ma'aunar hatsi da harkan kayan wato taguwa, da harkar sai da kayan wutan lantarnki da harkan wayoyin hannu da sauran su. Hakama akan samu wani bangare a kasuwa inda suke sai da dabbobi irinsu tumakai, awakai, shanu har dama Rakuma da tsuntsaye.
kiwo
gyara sasheita dai sana'ar kiwo kamar sana'ar noma ce.kiwo na kowa da kowane, matukar kana da sha'awa zaka iya yinshi. shi dai kiwo ba yaro ba tsoho, kowa kan iya yinshi. kiwo ba maza kadai aka sani ba har mata sukan taka rawa acikin sa.
Dillanci
gyara sasheDillanci sana'a ce ta [[Dattijai]] ta hanyar karban kayan mutane asayar masa, sannan shi me kayan ya biya mai sayarwa ladan aiki ko dawainiyya da yayi da kaya wurin sayar wa.
yadda akeyin Dillanci
gyara sasheidan Mallam bahaushe yana da kaya ko abin sayarwa yakanyi tallar kayan zuwa ga dillalai idan an samu mai siya sai a biya shi lada.a Wannan fannin dillali yakan wakilta mai kaya ta hanyan saida kayan sa.
Kwadago
gyara sasheKwadago na nufin ayi aiki abiya  shine ake kira da kwadago. Kwadago aiki ake biya kadan anan take, ba kamar sauran ayyuka bane. kwadago aiki ne na yarjejeniya yin wani aiki na karfi sanan abiya kadan aikin da aka gudanar. aikin kwadago ya shafe aikin Gona , Gini, da aikin albashi.
Ire-iren Aikin Ƙodago
gyara sasheAkwai ayyukan Gona kamar misalin sharan  gona, ko shuka har dama Noma, a wani bangare Akwai ayyukan na Gida kamar su Gini, da sauran su.
Masu aikin ƙwadago
gyara sasheMafi yawancin masu aikin ƙwadago babu kamar [[Almajirai]] ko yan [[ci rani]] sune sukafi yin wannan aiki.
Aikatuta
gyara sasheAikatau da kwadago duk tafiyar su daya ne, sai dai bamban cin su kadan ne, maza suke kwadago mata su kan yi aikatau a gidaje .
Ire-iren aikatau
gyara sasheAikatau a gida ake yi musamman matar karkara da ake dauko su daga ƙauye domin taya mutanen birni aiki sannan a biya su ladan wannan aiki, aikatau na gida bai wuce [[wanke-wanke]]da shara, ko surfe, ko aike na yau da kullum, ko [[sukola]], ko renon ƴaƴan.
Jima
gyara sasheMe ake kira da jima, aiki ne na sarrafa fatu dabbobin ta yadda masu sana'ar dukanci suke buƙatar, majemi yakan fitar da gashin dabbobin ya gyara har takai da yayi laushi awurin gudanar da aiki.
Kayan aikin jima
gyara sasheSun hada da [[gabaruwa]] da Ruwa da rika, san nan akwai [[kwatanta]] da awartaki da dutse har da gungume eche, da sauran su.
Fawa
gyara sasheFawa sana'a ce ta gado ga irin gida na mahauta, sana'ar fawa ta samo asali tun zamanin Annabawa da manzannin, sannan akwai alfanu  sosai cikin wannan sana'a, mahauci ya kan tafi kasuwa domin sayar dabba da zai yanka domin sayarwa al'umma Nama . mahauci yakan tanaji jallin sa da zai ishe shi yin wannan sana'a, yakan sayi dabba kamar su tumakai, ko awakai, ko saniya domin al'umma su ci.
Al'adu mahauci
gyara sasheA al'adar mahauci akwai su da karamci, sanan suna da al'ada idan sun samu ƙaruwa su kanyi bukukuwan su na hawan ƙaho saniya da dai sauransu.
Wanzamci
gyara sasheSana'ar wanzamci sana'ar kasar Hausa ce tun tale-tale, wanzami ya kanyi aski ga manjya dattijai ko saraki kai har ma da jarirai idan an samu ƙaruwar, san nan yana cire belu-belu da shayi wato kachiya da Ƙaho har ma da ɓalli-ɓalli.