Samuel Aruwan
Samuel Aruwan (an haife shi 10 ga Mayu 1982) ɗan jarida ne, kuma Kwamishinan Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna daga shekara ta 2019 zuwa 2023. Ya yi kuma Kantoma da Kwamishinan birnin Kaduna daga shekara 2023 zuwa 2024. Yayi aiki kuma matsayin Babban Mai Bada Shawara akan yadda labarai harwa yau kuma mai magana da yawun gwamna daga 2015 zuwa 2019. A yanzu haka kwarare ne a harkan tsaro.
Samuel Aruwan | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Jahar Kaduna, 10 Mayu 1982 (42 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Sana'a |
Tarihi
gyara sasheSamuel Aruwan haifaffen gundumar Tudun Wada, dake karamar Hukumar Kaduna ta Kudu a Jihar Kaduna, Najeriya. Shi kwararren ɗan jarida ne wanda yake da ƙwarewa shekaru goma kafin ya shiga aikin gwamnati a 2015. Aruwan ya kammala karatun digiri a fannin sadarwa a kwalejin kimiyya da fasaha da ke Kaduna. A shekarar 2012, ya halarci horon horar da 'yan jarida na binciken Afirka a jami'ar Witwatersrand, Afirka ta Kudu. Ya kasance daya daga cikin ‘yan jaridar Najeriya da aka horar kan yadda za a dakile tsattsauran ra’ayin addini a Tony Blair Institute for Global Change, London a 2014 da kuma a Drew University’s Institute on Religion and Conflict Transformation, New Jersey in 2016. A yanzu haka dalibi ne a jam'iyar Ahmadu Bello da ke Zariya.
Manazarta
gyara sashehttps://www.channelstv.com/tag/samuel-aruwan/ http://www.citypeopleonline.com/meet-gov-el-rufais-tireless-spokesman/ https://punchng.com/el-rufai-makes-spokesman-security-commissioner/