Samfuri:Mukalar mu a yau/8
Rahama Sadau (7 Disamba, 1993), an haifeta ne a garin Kaduna, jaruma ce a Kannywood da kuma Nollywood a Najeriya, kuma ta kasan ce mai shirya fina-finai. Rahama tayi wasan gasan rawa a lokacin da take yarinya kuma a lokacin tana makaranta. Ta yi suna ne a ƙarshen 2013 bayan ta shiga masana'antar fim ɗin Kannywood tare da fim ɗinta na farko Gani ga Wane. Rahama ta fito a cikin finafinan Najeriya da yawa a cikin fina finan Hausa da turanci, kuma tana ɗaya daga cikin yan wasan kwaikwayon Najeriya da ke iya magana da harshen Hindi sosai, Ita ce ta lashe lamban girma na kyautar Actress a (Kannywood) na Kyautar City People Entertainment Awards a shekarar 2014 da 2015, Ta kuma sami kyauta mafi tsoka.