Sam Aryeetey
Sam Greatorex Aryeetey (an haife shi a ranar 23 ga watan Agusta 1929 ko 1927)[1] ɗan Ghana ne mai shirya fina-finai, kuma daraktan fina-finai kuma marubuci.[2] Sau da yawa ana yaba masa a matsayin daraktan fim ɗin farko na Ghana, No Tears for Ananse.[3]
Sam Aryeetey | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Accra, 1929 (94/95 shekaru) |
Sana'a | |
Sana'a | marubin wasannin kwaykwayo da darakta |
IMDb | nm0038173 |
Rayuwa
gyara sasheAn haifi Sam Aryeetey a ranar 23 ga watan Agusta, 1929, a Accra. Ya yi karatu a Accra Methodist Boys School da Achimota School. Daga cikin ɗalibai na farko a makarantar horar da fina-finai na Accra ga mutanen yammacin Afirka wanda Sashen Fina-Finan Mallaka suka kafa a shekarar 1948, Sam Aryeetey ya shiga sabon sashin fina-finai na Gold Coast ƙarƙashin Sean Graham. A shekarar 1952 ya koma aiki a matsayin edita a Ingila. [4]
A cikin shekarar 1963, Sam Aryeetey ya koma Ghana don yin aiki da Kamfanin Masana'antar Fina-finai ta Ghana (GFIC). [5] No Tears for Ananse, wanda Aryeetey ya rubuta kuma ya jagoranta, shine farkon samar da GFIC. Ya dogara ne akan wasan kwaikwayo na Joe de Graft 's Ananse da Gum Man', labari game da Trickster Ananse.
A shekara ta 1969, Sam Aryeetey ya zama manajan darakta na GIFC. Manthia Diawara ya bayar da hujjar cewa, ta hanyar zabar turawa aiki maimakon 'yan Afirka don "yi fina-finai ga Ghana".
Ayyuka
gyara sasheFina-finai
gyara sashe- (as editor) I Will Speak English, 1954
- (as editor) Mr. Mensah Builds a House, 1955
- (as editor) The Welfare of Youth, Editor
- (as editor) Sporting Life, 1958
- (as producer) Hamile the Tongo Hamlet, 1964
- (as director) No Tears for Ananse, 1965 or 1968
- (as writer) The African Deal, 1973
Littattafai
gyara sashe- ‘’Harvest of Love’’, 1984
- ‘’Other Side of Town’’, 1986
- ‘’Home at Last’’, 1996
Manazarta
gyara sashe- ↑ Raph Uwechue (1991). Africa Who's who. Africa Journal Limited. p. 220. ISBN 978-0-903274-17-3.
- ↑ "Aryeetey, Sam, 1927- - LC Linked Data Service: Authorities and Vocabularies | Library of Congress". id.loc.gov. Retrieved 2019-11-17.
- ↑ Ian Aitken (2016). Colonial Documentary Film in South and South-East Asia. Edinburgh University Press. p. 59. ISBN 978-1-4744-0721-2.
- ↑ Tom Rice, Gold Coast Film Unit, ‘’Colonial Film: Moving Images of the British Empire’’, June 2010.
- ↑ Ghana Year Book, 1978, p.245.