Sadiq Saleh
Sadiq Saleh, Shahararren matashin mawakin Hausa ne mai zuwa, wanda tauraruwarsa ke haskawa tun karshen shekarar 2022. An haifi matashin mawakin ne a Maiduguri wanda yake babban birnin jihar Borno, dake arewa maso gabashin Najeriya. Sadiq Saleh yana da kyakykyawan murya mai ban sha'awa, wanda ya sa ya bambanta a cikin takwarorinsa na masana'antar.
Kuma wakar mai suna “abun ya motsa” ta zama sanadin shahararsa a fadin Najeriya da ma duniya baki daya. A yanzu haka a arewacin Najeriya wakar Sadiq Saleh ita ce wakar da aka fi saurare a fadin masoya wakokin Hausa a kasar.
Wakokin Sadiq Saleh
gyara sashe- Wakar yabon manzon Allah ( S A W )
- Abin ya motsa
- Azuciya so yayi min rana
- Buri
- Idan so cuta ne
- Har abada
- Sai kallo
- Cousin farin ciki
- Farin ciki
- Korafi kalma guda
- Wazai deben kewa
- Gaskiyar lamari tukuycin kauna
- Tun bayan rabuwa
- Zuciya daso kyauta
- Darasul auwal
- In bake
- Ko wiya ko dadi
- Mai kishina