Sabon-Gari
Karamar hukumar Sabon Gari karamar hukuma ce a jihar Kaduna a Najeriya.[1] Yana daya daga cikin kananan hukumomin da ke cikin birnin garin Zariya sannan kuma daya ne daga cikin gundumomin masarautar kasar Zazzau . Birnin da koma qauye dogarawa, bomo, basawa, zabi, Samaru, kwari, Barashi, Machiya and Palladian. Majalisar karamar hukumar na karkashin jagorancin Alhaji Mohammed Usman. [2]
Sabon-Gari | ||||
---|---|---|---|---|
| ||||
Wuri | ||||
| ||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | |||
Jihohin Najeriya | Jihar Kaduna | |||
Tsarin Siyasa | ||||
Majalisar zartarwa | supervisory councillors of Sabon-Gari local government (en) | |||
Gangar majalisa | Sabon-Gari legislative council (en) | |||
Bayanan Tuntuɓa | ||||
Kasancewa a yanki na lokaci |
Yawan jama'a
gyara sasheKaramar hukumar Sabon Gari tana da yawan jama'a da kiyasin mutane 204,562. Garuruwan sun karbi bakoncin mutane daban-daban na kabilu daban-daban. Babban harshen da ake amfani da shi shi ne harshen Hausa yayin da Musulunci da Kiristanci su ne addinan da ake yi a tsakanin mutanen yankin.
Geography
gyara sasheMatsakaicin zafin jiki shine 32 ° C, tare da manyan yanayi guda biyu waɗanda suke bushe da damina.
Tattalin Arziki
gyara sasheKasuwanci wani muhimmin aiki ne na tattalin arziki na Sabon Gari inda yankin ya mallaki kasuwanni da dama irin su Samaru zariya da manyan kasuwannin Sabon Gari wanda ke jan hankalin dubban kwastomomi kamar saye da sayarwa. Gida ne na ɗalibai da ayyukan ilimi tare da ayyukan noma masu fa'ida.
Manazarta
gyara sashe- ↑ Mortimore, M.J (1970). Zaria and it's regions: A. Nigerian Savannah city and it's environs. Department of Geography, Ahmadu Bello University, zaria.
- ↑ "Three to die by hanging in Zaria". Vanguard News (in Turanci). 2020-03-10. Retrieved 2022-03-14.