Rumfa
Rumfa jam'in ta shine Rumfuna wata aba ce da ake yi a ƙauyuka don ajiye kayayyakin abinci babbar rumfa kenan, in kuma ƙarama ce a gida ana ajiye kayayyakin amfani kamar kwanoni da kwarya ƙorai da dai sauransu. Wani lokacin ma, ana zaunawa a ƙarƙashin rumfa don inuwa musamman lokacin zafi. Ƙaramar rumfa tanada turke huɗu, ita kuma babba ya danganta da yadda wanda yake yinta ya tsarata.
Anayin rumfa da itace a kafa su a kasa sai a sama a Shimfiɗa wasu daga nan sai a biyo da kara musamman karan dawa da na gero [1][2]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Rumfa". Hausadictionary.com.
- ↑ "Indiya: Rumfa ta fado kan masu bauta ta kashe mutum 14". BBC Hausa. 24 June 2019. Retrieved 30 August 2021.