Robert Emmanuel Pires (An haifeshi a ranar 29 ga watan Oktoba shekara ta alif 1973). Mai haraswa ne dan kasar Faransa kuma tsohon kwararren dan wasa a harkar tamaula.[4] Dan wasan yana daya daga cikin yan wasa mafi daraja a kungiyar kwallon kafa ta Arsenal.[5] Pires ya buga ma kungiyoyi na kasar Faransa, Metz da kuma Marseille. Sai ya tsallaka kungiyar kwallon kafa ta Arsenal kuma ya kafa tarihi kuma yaci kofina a kungiyar inda yaci gasar FA sai kuma babbar gasa ta kofin Premier League har sau 2. Daga ciki akwai guda daya wadda suka lashe ba tare da wata kungiya tayi nasara akan kungiyar tasu ba a shekarar alif 2003-2004.

Pires

Tsohon ɗan wasan kasar Faransa ya buga wasanni guda 79 tsakanin shekarar alif 1996 da kuma shekarar alif 2004 a kasar tashi ta Faransa. Kuma ya samu nasarar lashe gasar cin kofin duniya baki daya a shekarar alif 1998 da kuma gasar da aka buga ta Euro shekarar alif 2000. Dan wasan ya shigo cikin manyan yan wasa na shekara da PFA ta fitar a shekarar alif 2002-03, 2003-04. Kuma dan wasan ya samu nasarar lashe kyautar dan wasan shekara a gasar FIFA Confederation Cup wanda aka buga a a shekarar alif 2001. An karrama shi da kyautar FWA na shekara a shekarar alif 2001-02. Kuma dan wasan ya samu nasarar lashe kyautar dan kwallo mafi karancin shekaru da yafi kowa a gasar League 1 na shekarar alif 1995-96. Inda ya samu nasarar shiga a cikin FIFA 100 ta Pele. Haka zalika ya samu karɓuwa da magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal har suka zabe shi cikin jerin manyan yan wasa na ƙungiyar har yazo mataki na 6 daga cikin fitaccin yan wasa a tarihin kungiyar.[6]

Pires ya buga mafi yawancin wasannin shi a matsayin dan gaba na gefen dama kuma yana buga tsakiya domin kara ma yan gaba karfi. Daga karshe Pires ya zama cikin masu horaswa a kungiyar kwallon kafa ta Arsenal.[4]

Shekarun Baya

gyara sashe

An haifi Pires a garin Reims na kasar Faransa inda babansa ya kasance dan kasar Portugal, mamarsa kuma yar kasar Ostireliya ce.

Pires ya kasance yaya ne ga yara guda 2 inda ya shafe kusan yarintarshi da rigunan kwallo guda 2, daya ta kungiyar Benfica ce saboda babanshi masoyi ne a kungiyar. Dayar kuma rigar kungiyar kwallon kafa ta Real madrid ce. Pires be meda hankali sosai ba a makaranta saboda matsanancin halin da yake ciki na rashin jin yaren Faransanci kasancewar a gidansu anayin yaren Fotugalanci da kuma yaren Sifaniyanci.[8] Ya gado san kwallo ne daga wajan mahaifinsa Antonio wanda yayi wasa a kungiyar kwallon kafa ta Les Corpo a karamin wuri. Kuma duk ranar Asabar Pires din yana zuwa kallon wasan shi da dare. Yana dan shekara 15 yabar makaranta inda ya fara gina rayuwar sa ta kwallo inda yayi shekara 2 yana karatun digiri a garin Reims. Da matsawar mahaifiyarsa, Pires ya zauna a Reims din kuma sun kirashi bayan shekaru 4.[8]

Rayuwar Kungiya

gyara sashe

Faransa

Pires ya kammala karatu a makarantar wasanni ta Reims inda ya fara wasa a matsayin kwararren dan wasa a shekarar alif 1993 a wasan da suka fafata da kungiyar kwallon kafa ta Lyon. Bayan yayi shekaru guda shida ya samu nasarar zura kwallaye har guda 48 a cikin wasanni 162 inda yaci gasar Coupe De League. Dan wasan ya koma ƙungiyar ƙwallon kafa ta Olympic De Marseille a shekarar alif 1998 da jumillar kudi har £5m. Pires ya hade shekara biyu inda ya tsaya jiran tsammani. A shekarar shi ta farko a kungiyar kwallon kafa ta Marseille, kungiyar ta rasa gasar French division 1 a shekarar alif 1998-99 inda maki daya ya hanasu daukar gasar. Kuma kungiyar taje matakin karshe a gasar ta UEFA cup. Saidai sunyi rashin nasara a hannun kungiyar kwallon kafa ta Parma. A kakar da yayi ta 2 ta sanya shi yasha wahala sosai ciki da Kuma wajen fili hakan ya tilasta mashi barin kungiyar a karshen kaka ta shekarar.[9]

Arsenal

2000-01

Pires ya rattaba hannu a kungiyar kwallon kafa ta Arsenal a shekarar alif 2000 akan jumillar kudi £6m. Kungiyar kwallon kafa Arsenal din tasha gaban kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid da kuma Juventus a cikin takarar siyan dan wasan. Dan wasan ya maye gurbin Marc Overmars dan wasan da ya koma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta FC Barcelona akan jumillar kudi £25m cinikin da ya zama tarihi a kungiyar.[8] Ya fara buga wasa na farko a kungiyar a wasan da suka fafata da Sunderland a ranar 19 ga watan Ogusta shekarar alif 2000.[10] Pires ya kasance mutum na daban inda wasu magoya baya suke sukar shi akan ya rasa abubuwa masu yawa. A cewar su Premier League tana bukatar dan kwallo mai lafiya da kuma karfin jiki. Sai dai hakan bai sa dan wasan ta fusata ba ko nuna damuwa akan wannan batu na magoya baya. A hankali Pires ya fara sabawa kuma ya dawo da kokarin da yakeyi a kungiyar kwallon kafa ta Meitz inda yaci kwallon solo a wasan da suka fafata da kungiyar kwallon kafa ta Lazio a watan Oktoba shekara ta alif 2000-01 a gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai.[10] Bayan kwanaki kuma ya zura kwallo ta farko a gasar Premier league a wasan da suka doke kungiyar kwallon kafa ta West Ham United daci 2-1.[12]

A lokacin da yake wasa a kungiyar yana da dabi'ar zura kwallo a ragar abokan hamayya wato kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Hotspur inda ya zura kwallo a ragar Tottenham Hotspur din a cikin haduwa 8 da akayi.[13]

Haduwa ta farko da yayi da kungiyar anyi ta ne a ranar 31 ga watan Match shekarar alif 2001 inda kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta samu nasara daci 2-0.[14] Bayan wata daya kuma ya ƙara zurama kungiyar kwallo a raga a gasar FA da aka buga na matakin kusa da na karshe.[15] Saidai ƙungiyar tayi rashin nasara a wasan karshe daci 2-1 a wasan da suka fafata da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool inda dan wasan ya taimaka akaci kwallon da Freddie Ljumberg yaci.[16]

2001-02

A shekarar alif 2001-02 ya saba sosai da gasar Premier league kuma cikin shekarun akwai shekarar da ta fi kowace a wajanshi. Pires yaci kwallo mai ban sha'awa a wasan da suka fafata da kungiyar kwallon kafa ta Middlesbrough da kuma kungiyar kwallon kafa ta Astonvilla. A wasan Aston Villa sunyi wasa mai kyau tare da abokin wasanshi Ljumberg daga karshe ya sanya ma Schmeichel a raga.[17][18] Pires ya sake cin kwallo a wasan da akayi 1-1 a filin wasa na White Hart Lane. Inda ya shafe kakar wasa yana sa kwallo a ragar Tottenham.[19]

Ya jagoranci Teburi a cikin wadanda suka taimaka aka zura kwallo a raga a shekarar. Inda ya anshi kyautar karramawa ta kyautar dan wasan da yafi kowa ta FWA. Kuma ya samu nasarar lashe gwarzon dan wasan da yafi kowa a kungiyar Kwallon kafa ta Arsenal na shekarar. Inda kungiyar ta lashe gasar ta Premier.[20] Pires ya taimaka ma abokin aikinsa wato Denis Berkamp inda yaci kwallo mai kyau ta sanyawa a tarihi a wasan da suka buga da kungiyar kwallon kafa ta Newcastle. Sai dai satin da ya biyo sun sake karawa da kungiyar a gasar FA inda dan wasan yaji rauni a cinyarsa (amma yaci kwallo tun farkon wasan kafin ya fita).[22] Hakan yasa dan wasan bai buga wasan karshe da aka buga a gasar FA da kuma gasar kofin duniya da aka buga a shekarar alif 2002 da kasar Faransa.[23]

2002-03

Bayan jinya da Pires yasha, dan wasan ya dawo a watan Nuwamba shekarar alif 2002. Inda yazo a matsayin dan benci a wasan da suka fafata da kungiyar kwallon kafa ta AJ Auxerre a gasar kofin zakarun nahiyar Turai.[24] Duk da cewa abin yazo mashi da wahala, amma ya dawo ganiyarsa har yaci kwallaye 14 cikin wasanni 20 da ya buga a gasar Premiership daga cikin kwallayen, yaci kwallaye 3 ringis a wasa daya a wasan da suka buga da kungiyar kwallon kafa ta Southampton a ranar da tafi mashi dadi a shekarar.[25] Sauran kwallayen kuma yaci 2 a karawar da sukayi da kungiyar kwallon kafa ta Fulham da kuma kwallo ta mintin karshe da ta ba kungiyar nasara a filin wasa na White Hert Lane.[26][27] An zabi dan wasan a matsayin dan wasan da yafi kowa a gasar Premier League na shekarar a watan Fabrairu shekarar alif 2003. Pires ya kammala shekarar inda yaci kwallo mai bada nasara a matakin karshe na gasar FA da kungiyar kwallon kafa ta Southampton.[26]

2003-04

Yazama cikin yan wasan kungiyar masu wahalar tarewa inda sukaci gasar Premier League a shekarar alif 2003-04. Kungiyar ta buga duka wasannin ta da ta buga a gasar. Inda suka zama kungiya ta farko a tarihin gasar tun bayan shekaru 115. Pires da abokin wasan shi wato Thierry Henry sune suka zama taurari kuma kwari sannan fitattu a cikin kungiyar ta Arsenal inda su biyun suka zura kwallaye 57 a dukkan gasannin da suka buga.

Pires ya fara a rashin sa'a inda yaci kwallo daya da yaci a wasan da suka fafata da kungiyar kwallon kafa ta Everton a watan Oktoba.[29] Amma yaci kwallo mai kyau a wasan Liverpool a filin wasa na Anfield farkon shekarar shi.[30]. Pires ya nuna ma magoya baya basirar dake gareshi da kuma hikima da iya jefa kwallo a raga musamman kwallayen da ya zura a ragar Liverpool, Leeds da kuma kungiyar Bolton Wanderers. Yaba mutane mamaki sosai inda ya yanki Claude Makalele kuma ya shiga da ita cikin layin 18 inda yayi waje da Gallas da kuma John Terry. Hakan yaba Patrick Viera damar yin arba da mai tsaron ragar kuma yaci kwallon inda aka tashi 2-1.[31]

Wannan ranar ta Premier League ta nuna alamun nasara ta lashe gasar saboda kasa yin nasara da kungiyar kwallon kafa ta Man Utd tayi akan Leeds United wanda aka buga a rana daya da wasan Arsenal. Hakan yaba kungiyar kwallon kafa ta Arsenal damar bada tazara kuma suka samu kwarin gwuiwar cin gasar lig.[32]

Kungiyar bata sabko bisa tuburi ba tun farkon gasar har zuwa karshen shekarar. A gasar zakarun Turai a matakin kusa da na kusan karshe wasan farko da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea. A wasan Pires yayi nasarar sanya ma kwallo kai a gaban John Terry inda kwallan ta shiga cikin raga. Sai dai kungiyar tayi rashin nasara daci 2-1 inda tayi waje a gasar. Haka zalika Pires ya zura kwallo a ragar kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Hotspur gida da waje. Dan wasan yana da kwarewa sosai idan yana fafatawa da kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Hotspur din. Yaci kwallo a wasan da akayi 2-2 da kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Hotspur. Anan ne Arsenal din ta ɗauki kofin lig.[34][35] Pires ya gama shekarar da kwallaye 14 ya kuma taimaka anci kwallo 7. Shine dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal wajan cin kwallaye (bayan Thierry Henry). Kuma yana cikin jerin yan wasa da suka fi kowa taimakawa akaci kwallo a shekarar. Inda yake a mataki na 2 bayan Denis Berkamp.[36]

2004-05

A shekarar alif 2004-05 Pires ya kare a mataki na 4 cikin jerin wadanda sukafi kowa cin kwallo a shekarar. Pires yana mataki na 3 cikin jerin mafiya cin kwallayen inda yake bayan Thierry Henry da kuma dan kwallon kungiyar kafar ta Crystal Palace mai suna Andrew Johnson.[36] Pires ya kara samun kyautar maratayi a gasar ta kofin FA. Har ya samu nasarar jefa kwallo a wasan kusa da na karshe da kungiyar kwallon kafa ta Blackburn Rovers. Sai kuma suka hadu da kungiyar kwallon kafa ta Manchester United inda kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta samu nasara da bugun daga kai sai mai tsaron raga.[38]

2005-06

Lokacin shekarar 2005-06 Pires ya fara shekarar a rashin kokari. Yan wasa irinsu Freddie Ljumberg da Alexander Hleb da kuma Antonio Reyes sune ake sakawa suna buga gefen. Shekarar na ci gaba dan wasan yana kara dawowa cikin ganiyarsa har ya zura kwallo a ragar abokan hamayya ta kungiyar kwallon kafa ta Manchester City har ya jawo bugun daga kai sai mai tsaron raga kuma yaba abokin aikinsa wato Thierry Henry inda ya zudda kwallon kuma haka zalika aka barar da bugun daga kai sai mai tsaron ragar.[39] A shekarar ne yaci kwallo a filin wasa na White Hart Lane inda ya zura kwallo (ta 8 a wasan karshe da suka buga da kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Hotspur). Kuma ya taimaki kungiyar a wasan canjaras da suka buga da kungiyar wigan Athletic 1-1 inda ya ramo kwallon a minti na karshe.[40][41]

Pires ya zama abun mamaki da kokarin da yayi a wasan da kungiyar tasu ta fafata da kungiyar kwallon kafa ta Juventus inda ya samu nasarar yankar Viera a wasan kuma ya jefa ma abokin aikinsa Thierry Henry shi kuma yaba saurayin dan wasa wato Fabrigas shi kuma yaci kwallo ta farko ga kungiyar shine karo na farko da ya sanya Viera talla. Wasan ya tashi 2-0 nasara ga kungiyar kwallon kafa ta Arsenal.[42]

Pires ya buga wasanshi na karshe da kungiyar kwallon kafa ta Barcelona a gasar zakarun nahiyar Turai a wasan karshe da aka buga a garin Paris inda kungiyar tayi rashin nasara daci 2-1. An fitar da dan wasan tun mintina 18 da fara wasan inda aka sallami mai tsaron ragar Arsenal wato Jens Lehmann. Inda mai tsaron raga wato Aluminia ya anshi Pires.[43] Arsenal sun sha wahala a wasan bayan cire dan wasan kuma shima kocin Kungiyar wato Arsene Wenger beyi shawarar da ta dace ba.

Barin Wuri

A lokacin shekarar alif 2005-06 Pires ya kara kulla yarjejeniya da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal akan kwantiragi har na tsawon shekaru 2 inda ya girmama dokar kungiyar ta ajiye yan wasa guda 30. An kara ma dan wasan watanni 6 daga cikin kwantiragin dan wasan inda ya raba gari da kungiyar a shekara ta alif 2006 ga watan June.[]

A watan Mayu shekara ta alif 2006 dan wasan ya amince da tayi na kungiyar kwallon kafa ta Villa Real inda suka daidaita da dan wasan.[45] Ya koma ƙungiyar bayan haduwa da yayi da sabuwar kungiyar tashi a gasar zakarun nahiyar Turai kuma ya samu nasarar yin waje da sabuwar kungiyar tashi a matakin wasan kusa da na karshe.[]

Daya daga cikin dalilan da yasa Pires yabar kungiyar kwallon kafa ta Arsenal a yanda dan wasan ya fada yace bashi bane zabi na farko ba a karkashin jagorancin mai horaswa na kungiyar wato Arsene Wenger. Pires yana da wata karin magana da take cewa "an bani kunya a cikin wannan shekarar misali ace nine ke zaune a benci harna tsawon lokaci" Pires yana tunanin cewa fidda shi da akayi a wasan karshe na gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai ya ji a ranshi cewa kamar kimar shi ta zube a idon kocin dan asalin Kasar Faransa wato Arsene Wenger. Pires yana tunanin mai horaswar be yarda dashi ba. Wannan shi ne dalilin da ya kara masa kwarin gwuiwar raba gari da kungiyar.[]

A wasan da akayi da kungiyar kwallon kafa ta Wigan Athletic a ranar 11 ga watan Fabrairu shekarar alif 2007. Pires din ya samu karayar zuciya a wasan inda aka fidda shi a wasan. Dan wasan yace naji karayar zuciya a yayinda naga lamba ta bisa allo a matsayin canji. Na kasa yadda saboda bayan shekaru 6 a kungiyar, wasan karshe ta gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai a gaban duka iyalaina a garin Paris inda na zama gwarzon duniya saidai kuma hakan ya ƙare a mintina 12 kacal, wannan yana da wahalar dauka.[]

A ranar 11 shekarar alif 2008 magoya bayan kungiyar sun zabi dan wasan a mataki na 6 cikin jerin manyan yan wasa na ƙungiyar.[]

Villa Real

A watan Mayu shekarar alif 2006 Pires ya kulla yarjejeniya da kungiyar kwallon kafa ta Villa Real da yarjejeniyar shekara 2 a matsayin kyauta inda ya tsallake gwajin lafiya da akayi mashi a kungiyar. Tun daga lokacin da kungiyar kwallon kafa Arsenal din tayi waje da kungiyar kwallon kafa ta Villa Real a gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai Kocin kungiyar yasha alwashin cewa sai ya kawo daya daga yan wasan biyu ko Thierry Henry ko Pires. Daga karshe kuma yayi nasarar kawo Pires din.[43]

Pires yaci kwallansa ta farko a kungiyar a wasan da suka buga da kungiyar kwallon kafa ta Newcastle Inda sukayi canjaras inda wasan ya tashi 3-3 a ranar 5 ga watan Ogusta shekarar alif 2006. A ranar 18 ga watan Ogusta shekarar alif 2006 Pires ya samu mummunan rauni a kashinsa a wasan da suka fafata da kungiyar kwallon kafa ta Cadiz. Ya samu kulawa inda akayi mashi aikin tiyata a raunin da ya samu a jikin nashi. Dan wasan ya shafe tsawon watanni har 7 yana jinya a cikin kasar ta Sifaniya.

Pires ya samu lafiya har ya fara yin atisaye da kungiyar. Dan wasan ya buga wasanshi na 2 a kungiyar inda ya fito a matsayin dan benci a wasan da suka fafata da kungiyar kwallon kafa ta Real Sociedad wanda aka buga a ranar 17 ga watan Match shekarar alif 2007. Pires yaci kwallansa ta farko bayan dawowarsa daga jinya da yasha inda yaci kungiyar kwallon kafa ta Real Betis inda akayi canjaras a wasan inda aka tashi 3-3 a ranar 31 ga watan Maris shekarar alif 2007.

Bayan wasanni guda 3 daya buga a matsayin dan benci, ya fara buga wasan da aka fito dashi a cikin 11 din farko da aka fara dasu a wasan. Sun fafata da kungiyar kwallon kafa ta Barcelona wanda aka buga a ranar 22 ga watan Afrilu shekarar alif 2007 inda ya fara buda kwallo a raga yayin da suka doke kungiyar masu jan ragamar Teburin Laliga daci 2-0. Hakan yasa ya samu salama da hanashi daukar zakarun Turai da sukayi.[]

A ranar 13 ga watan Mayu shekarar alif 2007 a nasarar da suka samu inda suka fafata da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Osasuna kuma suka samu nasara daci 4-1. A wasan Pires yaci kwallo tun a minti na 7. Kungiyar taci gaba da matsawa cikin rukunin jerin kungiyoyin da zasu buga gasar turai. Kungiyar kwallon kafa ta Villa Real din ta kare a mataki na 5 inda Pires ya taimaka kungiyar sosai wajan cin kwallaye masu amfani wajan samun nasara. Kuma hakan yaba kungiyar damar hayewa domin buga gasar kofin Turai.[]

Lokacin shekarar alif 2007-08 ya maku tsakanin Juan Roman Requelme da Kuma masu ruwa da tsaki na kungiyar. Duk da lalacewar kungiyar, jagorancin Pires y taimaki kungiyar sosai wajan cinye wasanni 6 da suka yi cikin wasanni 8 din farko.

Wasan da sukayi da kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Jagoranci nashi da kuma basirar shi sun taimaka sosai wajan samun nasara a wasan inda dan wasan ya jawo bugun finareti guda 2 inda caftin na kungiyar wato Marcos Cena yaci kwallayen a raga.[]

Villa Real sun samu nasarar gamawa a mataki na 2 a gasar Laliga wanda hakan babbar nasara ce a kungiyar kuma shekarar ta shiga cikin kundin tarihin kungiyar. Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid itace ta samu nasarar lashe gasar a wannan shekarar sai kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta kare a mataki na 3.[49]

A shekarar alif 2009 Pires ya hadu da tsohuwar kungiyar shi ta Arsenal inda wasan farko ya shigo cikin minti na 70, a wasa na 2 kuma ya buga mintuna 90 cir a wasan inda kungiyar sa tayi rashin nasara a hannun tsohuwar kungiyar tashi daci 4-1 a duka wasannin saidai magoyan tsohuwar kungiyar tashi sun rera waka suna kiran sunanshi a duka haduwar da akayi.[]

A watan Mayu shekarar alif 2010 an sanar da shi cewar ya nemi sabuwar kungiyar da zai koma saboda kwantiragin shi ya ƙare kuma an kawo sababbin tsare tsare a kungiyar.[49]

Aston Villa

Pires ya dawo atisaye a filin atisaye na London Colney inda yake daukar horo tare da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal domin ya kara samun lafiya da kuma murmurewa.[50]

A watan Oktoba shekara ta alif 2010 wasu jaridu sun ruwaito cewa dan wasan zai jona kungiyar na wasu yan watanni sai dai daya daga cikin masu ruwa da tsaki na kungiyar ya ƙaryata labarin.

A ranar 16 ga watan Nuwamba shekarar alif 2010 Gerrad Houllier wato mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Aston villa ya gama tattaunawa da wakilan dan wasan.[52] a ranar 18 fa watan Nuwamba dan wasan ya kammala komawa kungiyar da kwantiragin wata 6 kacal.[53]

Manazarta

gyara sashe

https://en.wikipedia.org/wiki/Robert_Pires