Babban asibitin Randle babban asibitin jiha ne a gundumar Surulere a Legas, Najeriya. Cif Majekodunmi ne ya kafa shi don amfanin al’umma a shekarar 1964 kuma yana daya daga cikin asibitocin kula da lafiya na farko a Surulere.

Randle General Hospital
Wuri
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
JihaLagos
BirniLagos
Coordinates 6°30′30″N 3°21′26″E / 6.5084°N 3.3572°E / 6.5084; 3.3572
Map
Contact
Address 28 Benson St, Surulere, Lagos 101241, Lagos

Asibitin yana aiki tuƙuru, musamman a sashen haɗari da gaggawa.

Tarihi gyara sashe

An kafa wannan asibitin ne don bayar da kulawar lafiyar mata da yara, aikin hakora, aikin likita da tiyata da dai sauransu. Wani lokaci ana kiransa da Babban Asibitin Surulere.[1][2][3] Daraktan lafiya na asibitin Dr. Aduke Odutayo.

Asibitin ya bayyana jimlar marasa lafiya 6929 da suka ziyarci sashin hakori na tsawon watan Janairu zuwa Disamba a cikin shekara ta 2020.[4]

Manazarta gyara sashe

  1. "Randle General Hospital• Hospitals-Public• Surulere, Lagos". www.medpages.info. Retrieved 2022-02-22.
  2. "Randle General Hospital, Hakeem Habeeb Cl, Surulere 101241, Lagos". ng.africabz.com. Retrieved 2022-02-22.
  3. "Surulere General Hospital, Lagos". Hotels.ng Places. Retrieved 2022-02-22.
  4. "RANDLE GENERAL HOSPITAL DENTAL DEPARTMENT RECORDS INCREASED PATRONAGE". Lagos State Government. Retrieved 2022-02-22.