Ramesh Kumar Vankwani ( Sindhi رميش كمار وانكواني) ɗan siyasan Pakistan ne wanda ya kasance memba a Majalisar Dokokin Pakistan, daga watan Agustan 2018 zuwa watan Agustan 2023. Amma a cikin shekarar 2022 ya bar PTI. A baya ya kasance memba na Majalisar Dokoki ta ƙasa daga watan Yunin 2013 zuwa watan Mayun 2018 kuma memba na Majalisar lardin Sindh daga shekarar 2002 zuwa ta 2007.

Ramesh Kumar Vankwani
Member of the 14th National Assembly of Pakistan (en) Fassara

1 ga Yuni, 2013 - 31 Mayu 2018
District: reserved seats for minorities (en) Fassara
Member of the National Assembly of Pakistan (en) Fassara


District: reserved seats for minorities (en) Fassara
Rayuwa
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Addini Hinduism (en) Fassara
Jam'iyar siyasa Pakistan Muslim League (N) (en) Fassara

Ilimi & Fage gyara sashe

Vankwani ya mallaki digirin farko na likitanci da kuma digiri na farko na tiyata.[1] An haife shi a Islamkot, Tharparkar a cikin shekarar 1974, a cikin dangin Hindu na Sindhi .

Harkokin siyasa gyara sashe

Vankwani ya tsaya takarar kujerar Majalisar lardin Sindh a matsayin ɗan takara mai zaman kansa daga Mazaɓar PS-61 (Tharparkar-II) a babban zaɓen Pakistan na shekarar 2002, amma bai yi nasara ba. Ya samu ƙuri'u 34 sannan ya sha kaye a hannun ɗan takarar jam'iyyar National Alliance .[2] A cikin wannan zaɓen, an zaɓe shi a Majalisar lardin Sindh a matsayin ɗan takarar jam'iyyar Pakistan Muslim League (Q) a kan kujerar da aka keɓe ga 'yan tsiraru.[1] Ya kafa Majalisar Hindu ta Pakistan[3] a cikin shekarar 2005.[4]

An zaɓi Vankwani a Majalisar Dokokin Pakistan a matsayin ɗan takarar jam'iyyar Pakistan Muslim League (PML-N) a kan kujerar da aka keɓe ga 'yan tsiraru a babban zaɓen Pakistan na shekarar 2013 .[5][6]

Vankwani ya fito fili ne a cikin watan Satumbar 2014,[7] lokacin da aka cire shi tare da Rehman Malik daga jirgin da ya taso daga Karachi zuwa Islamabad saboda rashin shiga da suka yi wanda ya sa jirgin ya yi tsaiko.[8][9]

Vankwani Janairun 2018, an zaɓe shi a matsayin shugaban kwamitin ƙididdiga na Majalisar Dokoki ta ƙasa.[10] A cikin watan Afrilun 2018, ya bar PML-N kuma ya shiga Pakistan Tehreek-e-Insaf (PTI).[11]

An sake zaɓen shi a Majalisar Dokoki ta ƙasa a matsayin ɗan takarar PTI a kan kujerun da aka keɓe ga tsiraru a babban zaɓen Pakistan na shekarar 2018 .[12] Ya tsaya kyam da manufofin jam’iyyarsa ba tare da amincewa ba.

Duba kuma gyara sashe

  • Mahesh Kumar Malani
  • Majalisar Hindu Pakistan

Manazarta gyara sashe

  1. 1.0 1.1 "Welcome to the Website of Provincial Assembly of Sindh". www.pas.gov.pk. Retrieved 7 April 2018.
  2. "2002 Sindh Assembly election result" (PDF). ECP. Archived from the original (PDF) on 13 April 2018. Retrieved 7 April 2018.
  3. "56 candidates vie for 15 Hindu Council seats". The Nation. Retrieved 7 April 2018.
  4. "Pakistan Hindu Council loses an active member". www.thenews.com.pk (in Turanci). Retrieved 7 April 2018.
  5. "Women, minority seats allotted". DAWN.COM (in Turanci). 29 May 2013. Archived from the original on 7 March 2017. Retrieved 7 March 2017.
  6. "Is the NA apathetic towards minority issues?". DAWN.COM (in Turanci). 22 September 2014. Archived from the original on 8 March 2017. Retrieved 7 March 2017.
  7. "PML-N's minority lawmaker Ramesh Kumar formally joins PTI". Daily Pakistan Global. Retrieved 7 April 2018.
  8. "Two Pakistani Politicians Got Kicked Off a Plane by Furious Passengers". Time. 17 September 2014. Archived from the original on 19 January 2015. Retrieved 21 January 2015.
  9. "Pakistan Rehman Malik: Passengers force ex-minister off plane". BBC News. 16 September 2014. Archived from the original on 15 February 2015. Retrieved 21 January 2015.
  10. "Dr Ramesh Kumar elected chairman of NA Committee on Statistics". www.pakistantoday.com.pk. Retrieved 6 April 2018.
  11. "Big blow to PML-N as MNA Dr Ramesh Kumar joins PTI". www.thenews.com.pk (in Turanci). Retrieved 7 April 2018.
  12. Reporter, The Newspaper's Staff (12 August 2018). "List of MNAs elected on reserved seats for women, minorities". DAWN.COM. Retrieved 12 August 2018.