Ramata Ly-Bakayoko
Ramata Ly-Bakayoko (an haife shi 29 Yuni 1955)[1] Malamar ilimi ce ta ƙasar Ivory Coast kuma jami'iyyar gwamnati ce. Ta yi aiki a matsayin ministar ilimi mai zurfi da bincike na kimiyya ta Ivory Coast daga shekarun 2016 zuwa 2018. An naɗa ta Ministar Mata, Iyali, da Yara a cikin shekarar 2018. An naɗa ta mataimakiyar dindindin ta Cote d'Ivoire zuwa UNESCO tare da zama a Paris a ranar 8 ga watan Satumba, 2021.
Ramata Ly-Bakayoko | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Abidjan, 29 ga Yuni, 1955 (69 shekaru) |
ƙasa | Ivory Coast |
Karatu | |
Makaranta |
Paris Diderot University (en) Paris Descartes University (en) |
Harsuna | Faransanci |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan siyasa, Malami da university president (en) |
Employers |
Jami'ar Félix Houphouët-Boigny Jami'ar Félix Houphouët-Boigny (2012 - 2016) |
Kyaututtuka |
gani
|
Mamba |
Académie des sciences d'outre-mer (en) Académie Nationale de Chirurgie Dentaire (en) Ordre international des Palmes académiques du CAMES (en) La Conférence des Recteurs des Universités Francophones d’Afrique et de l’Océan Indien (CRUFAOCI) (en) |
Imani | |
Jam'iyar siyasa | Rally of the Republicans (en) |
Tarihin Rayuwa
gyara sasheAn haifi Ly-Bakayoko a Abidjan, Ivory Coast, a shekara ta 1955.[1][2] Ta sami digiri a aikin tiyatar hakori daga Jami'ar Paris Diderot a shekarar 1980 da kuma ilimin hakori daga Jami'ar Descartes na Paris a shekarar 1985.[2]
Ly-Bakayoko farfesa ce a fannin likitan hakora na yara.[3] Ta shugabanci sashin kula da ilimin hakora na yara a Jami'ar Cocody (yanzu Jami'ar Félix Houphouët-Boigny) a Abidjan, daga baya ta zama mataimakiyar shugabar tsangayar ilimin hakora, sannan ta zama mataimakiyar shugabar jami'a.[2] Daga shekarun 2012 zuwa 2016, Ly-Bakayoko ta kasance shugaba mace ta farko ta Jami'ar Félix Houphouët-Boigny. A matsayinta na shugaba, ta haɓaka Cibiyar Kimiyya da Ƙirƙira a Bingerville, gida ga shirin Cutar Epidemiology na Yammacin Afirka (WAVE).
Ly-Bakayoko ta yi aiki a matsayin Ministan Ilimi mai zurfi da Bincike na Kimiyya daga shekarun 2016 zuwa 2018, ta gaji Gnamien Konan. Ita ce mace ta farko da ta rike wannan matsayi. A cikin shekarar 2018, an naɗa ta Ministar Mata, Iyali, da Yara.[4]
Kyaututtuka da karramawa
gyara sasheA cikin shekarar 2018, Ly-Bakayoko ta zama 'yar ƙasar Ivory Coast ta farko na Faransa Académie des sciences d'outre-mer. A cikin shekarar 2019, an ba ta digirin girmamawa daga Jami'ar Franche-Comté ta Faransa.[2][5]
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 Douce, Sophie (2017-12-20). "Q&R : La Côte d'Ivoire en première ligne sur le climat". SciDev.net (in Faransanci). Retrieved 2020-02-09.
- ↑ 2.0 2.1 2.2 2.3 "L'université de Franche-Comté décerne le titre de Docteur Honoris Causa au Pr Ramata Bakayoko-Ly". maCommune.info (in Faransanci). 2019-12-18. Retrieved 2020-02-10.
- ↑ "Ramata Ly-Bakayoko, première Ivoirienne à l'Académie des sciences d'outre-mer de Paris". Le Monde (in Faransanci). 2019-03-08. Retrieved 2020-02-10.
- ↑ Ouattara, Lacinan (2019). "Côte d'Ivoire : Un nouveau Gouvernement avec 42 ministres et 7 Secrétariats d'Etat". RTI (in Faransanci). Archived from the original on 2019-10-16. Retrieved 2020-02-15.
- ↑ "Pr Bakayoko-Ly Ramata fait Docteur Honoris Causa de l'université Franche-Comté de France". Agence Ivorienne de Presse (in Faransanci). 2019-12-18. Archived from the original on 2020-02-15. Retrieved 2020-02-10.