Radha Poonoosamy
Radha Poonoosamy ( Tamil : ராதா பொன்னுசாமி படையாச்சி) (née Padayachee, 18 na Satumba 1924 - Janairu 2008), yar siyasa ce ta Mauritius, ministar mata ta farko akasar, kuma minista mace ta farko.
Radha Poonoosamy | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 18 Satumba 1924 |
ƙasa |
Moris Afirka ta kudu |
Mutuwa | ga Janairu, 2008 |
Karatu | |
Makaranta | Jami'ar Natal |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan siyasa |
Imani | |
Jam'iyar siyasa | Indian National Congress (en) |
An haifi Radha Padayachee a ranar 18 ga Satumba 1924 a Durban, a Afirka ta Kudu. [1] An haife ta acikin dangin zuriyar Indiyawa.
Ta yi karatu a Jami'ar Natal, inda ta kasance "mai adawa da wariyar launin fata", kuma ta zama memba na Majalisar Dalibai na Majalisar Dokoki ta Indiya, wanda yake yaki da wariyar launin fata ta Indiyawa a Afirka ta Kudu. Ta ci gaba da zama shugabar sashin mata, sannan kuma memba a kwamitin zartarwa na jam'iyyar ANC. [2]
Ta auri likitan Dr. Valaydon Poonoosamy, kuma sun zauna a garin shMauritius a 1952. Ta zama 'yar ƙasa, kuma ta ci gaba da gwagwarmayanta a can cikin Jam'iyyar Labour ta Mauritius.
A shekara ta 1975, an zabi Poonoosamy a matsayin 'yar majalisa, inda ta zama ministar mata ta farko a kasar, ministan farko da ke kula da ma'aikatar harkokin mata, kuma ta taimaka wajen samar da dokokin yaki da wariyar jinsi.