Rabi'u Daushe
Rabi'u Ibrahim Daushe Jarumin barkwanci ne ɗan Najeriya daga masana'antar kannywood, ya shahara da sunan Daushe ko Daushe mai dabaibayi, ya shahara sosai a matsayin ɗan wasan barkwanci a masana'antar fina-finan Hausa.
Rabi'u Daushe | |
---|---|
Rayuwa | |
ƙasa | Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | jarumi |
Tarihin rayuwa
gyara sasheRabi'u daushe ɗan asalin jihar kano ne, ƙaramar hukumar wudil, an haifeshi A jihar kano Najeriya. Daushe yana ɗaya daga cikin fitattun jaruman barkwanci a masana'antar Kannywood, ya samu shedar kammala makarantar firamare da sakandare duk a jihar kano, kafin ya haɗa wani wasan kwaikwayo na kulob ɗin daushe malami ne a wata makarantar islamiyya ta nurul huda kuma yana koyar da karatun addinin musulunci, kuma primary wudil na musamman inda shima yake koyar da harshen hausa. [1]
Daushe
gyara sasheRabi'u daushe ya samo sunan sa na farko ne a wasan kwaikwayo na wasan kwaikwayo, a lokacin wasan kwaikwayo na kulob a jihar bauchi, ɗaya daga cikin daraktan nasa ya kira dukkan membobinsa ya tambaye su game da sunan lakanin da kowa ke so kafin wasan kwaikwayo ya fara, Rabi'u Ibrahim ya zabi "Daushe Mai Dabaibayi" a matsayin lakabin wasan kwaikwayo, tun kafin ya haɗe masana'antar Kannywood.
Aiki
gyara sasheRabi'u Ibrahim daushe shi ma ɗan kasuwa ne, baya ga wasan kwaikwayo, yana sana'ar dinki, sayar da tufafi, da kasuwancin kasa, kusan yana da fiye da nau'ikan kasuwanci 10, Shi ne hadin gwiwa na farko da Amina sannan kuma daga baya yana haɗa Hamdala wanda ya mallaki Marigayi Rabilu Musa Ibro, daushe ɗan fari ne daga cikin danginsa sannan kuma yana da kanne 11 maza da mata, kusan duk nauyinsu ya dauke su.
Rabi'u Ibrahim daushe ya kasance gwarzon dan wasan barkwanci a
Fina-finai
gyara sashe- Aljanar Dan Auta
- Alkalin Kauye
- Andamali
- Dan Auta Amalala
- Garbati
- Hanyar Kano
- Hawaye Na
- Ibro Ba Sulhu
- Jam Baki
- Jamila Mai Wasa Da Kura
- Karfen Nasara
- Tsohon Lauya
- Haka
Iyali
gyara sasheRabi'u Ibrahim daushe ya auri kyakkyawar matar sa shekarun baya kuma Allah ya albarkace su da kyawawan yara guda uku, Bashir, Fatima da Ibrahim Rabi'u Ibrahim Daushe.