Proscovia Margaret Njuki
Proscovia Margaret Njuki injiniyar lantarki ce kuma ma'aikaciyar gwamnati. Daga ranar 24 ga watan Nuwamba, 2016, tayi aiki a matsayin shugabar hukumar gudanarwar Kamfanin Lantarki na Uganda Electricity Generation Company Limited (UEGCL).[1] Ta maye gurɓin Stephen Isabalija, wanda aka nada babban sakatare a ma'aikatar makamashi da ma'adinai ta Uganda.[2]
Proscovia Margaret Njuki | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 25 ga Yuni, 1951 (73 shekaru) |
Mazauni | Kampala |
Karatu | |
Makaranta |
Makarantar Sakandare ta Gayaza Jami'ar Nairobi |
Sana'a | |
Sana'a | injiniyan lantarki, civil servant (en) da scientist (en) |
Tarihi da ilimi
gyara sasheAn haife ta a ranar 25 ga watan Yuni 1951 'ya ce ga Reverend da Mrs. Benoni Kaggwa-Lwanga. Ta halarci makarantar sakandare ta Gayaza don karatunta na O-Level da A-Level. Ta yi karatu a Jami'ar Nairobi, inda ta kammala karatun digiri na farko a fannin injiniyanci na lantarki a shekarar 1974, mace ta farko 'yar Uganda da ta kammala digiri a matsayin injiniya.[3]
Sana'a
gyara sasheBayan kammala karatunta a Nairobi, ta koma Uganda ta fara aikin injiniyanci na sadarwa a gidan talabijin na ƙasa na lokacin, Uganda Television (UTV). Ta tashi cikin matsayi kuma a cikin shekarar 1994, an naɗa ta shugabar sabis na injiniyanci na UTV. A shekara ta 1995, an nada ta Kwamishina na UTV.[3] Kafin ta zama shugabar hukumar ta UEGCL, ta yi aiki a matsayin mamba a wannan hukumar, ƙarƙashin jagorancin Dr. Stephen Isabalija.[2][4]
Sauran nauye-nauye
gyara sasheIta ce wacce ta kafa kungiyar Injiniyoyin Mata, Fasaha da Masana Kimiyya a Uganda, tun a shekarar 1989. Har ila yau, mamba ce a Cibiyar Injiniyoyi masu ƙwarewa a Uganda kuma ta yi aiki a majalisar zartarwa daga shekarun 1990 har zuwa 1993.[3]
Na sirri
gyara sasheA shekarar 1977 ta auri Samwiri HK Nnjuki kuma tare su ne iyayen 'ya'ya mata biyu da namiji ɗaya.[3]
Duba kuma
gyara sashe- Irene Muloni
- Monica Azuba Ntege
- Miriam Muwanga
Manazarta
gyara sashe- ↑ Muhame, Giles (24 November 2016). "Eng Njuki Appointed UEGCL Board Chairperson". Kampala: Chimpreports Uganda. Retrieved 21 June 2017.
- ↑ 2.0 2.1 UEGCL (2 February 2017). "Dr. Stephen Robert Isabalija handed over to Eng. Proscovia Margaret Njuki, the Chairperson ship of UEGCL". Kampala: Uganda Electricity Generation Company Limited (UEGCL). Archived from the original on 9 November 2017. Retrieved 21 June 2017.
- ↑ 3.0 3.1 3.2 3.3 Elizabeth Sleeman (2002). The International Who's Who of Women 2002: The Biography of Proscovia Margaret Njuki. Psychology Press. p. 408. ISBN 9781857431223. Retrieved 21 June 2017.
- ↑ "Electricity Generation Company UEGCL sees rare profits in 2015". The Independent (Uganda). Kampala. 26 September 2016. Retrieved 21 June 2017.