Prince James Uche
Prince James Uche ya kasance sananne kuma ana sha'awar shi a masana'antar fina-finai ta Nollywood. Prince ya shafe shekaru biyu yana fama da ciwon suga, makanta, hawan jini, da matsalolin koda kafin ya rasu a watan Maris na 2017.[1][2] Kafin rasuwarsa, Uche zai yi balaguro ne a ranar Asabar bayan da aka tara jimillar Naira miliyan 15 domin jinyar sa a kasashen waje ta hanyar gudummawar da wasu ’yan Najeriya masu kishin kasa ciki har da Gwamna Okezie Ikpeazu na Jihar Abia suka bayar.[3]Tauraron ya fito a fina-finan Nollywood kamar Coronation, Lost Kingdoms, da Igodo.[4]
Manazarta
gyara sashe- ↑ https://dailypost.ng/2017/03/08/breaking-nollywood-actor-prince-james-uche-dead/
- ↑ https://www.nairaland.com/3671261/biography-life-death-nollywood-actor#54396684
- ↑ https://www.premiumtimesng.com/entertainment/nollywood/225607-nollywood-actor-prince-james-uche-dead.html?tztc=1
- ↑ https://yen.com.gh/60441-20-actors-and-actresses-who-died.html