Philip Nnaemeka-Agu

Malamin shari'a na Najeriya

Philip Nnaemeka-Agu (1928-2011) masanin shari'a ne a Najeriya wanda ya kasance mai shari'a a kotun daukaka kara ta tarayya. Ya kasance Kwamishinan Shari’a na Jihar Gabas ta Tsakiya (1970 - 1972) da kuma shari’a a Kotun Koli ta Najeriya daga 1987 zuwa 1993.