Pedro (an wasan ƙwallon ƙafa, an haife shi a shekara ta 1987)

Pedro Eliezer Rodríguez Ledesma (an haife shi ne a ashirin da takwas 28 ga watan Yuli 1987), wanda aka sani da Pedro haifaffen dan qasar sipaniya, ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na ƙasar Sipaniya wanda ke taka leda a matsayin ɗan wasan gaba ko na gefe hagu da dama winger na ƙungiyar Serie A ta Lazio a qasaritaliya .

Pedro (an wasan ƙwallon ƙafa, an haife shi a shekara ta 1987)
Rayuwa
Cikakken suna Pedro Eliezer Rodríguez Ledesma
Haihuwa Santa Cruz de Tenerife (en) Fassara, 28 ga Yuli, 1987 (37 shekaru)
ƙasa Ispaniya
Harshen uwa Yaren Sifen
Karatu
Harsuna Yaren Sifen
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
  FC Barcelona C (en) Fassara2005-20077111
  FC Barcelona Atlètic (en) Fassara2007-20095116
  FC Barcelona2008-201520458
  Spain national under-21 association football team (en) Fassara2008-200820
  Spain men's national football team (en) Fassara2010-20176517
  Chelsea F.C.2015-202013729
  A.S. Roma (en) Fassara2020-2021275
  SS Lazio (en) Fassara2021-unknown value8714
 
Muƙami ko ƙwarewa Ataka
Lamban wasa 9
Nauyi 62 kg
Tsayi 169 cm
Kyaututtuka
Pedro Eliezer Rodríguez Ledesma a wasan da suka fafata da napoli

Pedro ya ci wa Barcelona kwallaye har casain da tara 99 a wasanni guda dari uku da ashirin da daya 321 da ya buga a duk gasa a qungiyar qwallon qafa ta Barcelona daga shekarai 2008 zuwa 2015. A lokacin kakar shekarai 2009–10, ya zama dan wasa na farko a tarihi da ya zira kwallaye a kowace gasa ta qungiyar a cikin kaka guda da kuma a cikin shekara guda. Ya koma Chelsea ne a shekara ta 2015 inda ya zura kwallaye 43 a wasanni 206 sannan ya taimakawa kungiyar ta lashe gasar Premier a shekarar 2017 da kofin FA a 2018 da kuma UEFA Europa League a shekarar 2019. Ya koma kulob din Serie A Roma a shekarar 2020 kuma ya koma abokan hamayyarsu na birnin Lazio a 2021.

Pedro ya wakilci qasar tasa ta Sipaniya a gasar cin kofin duniya na FIFA guda biyu da kuma gasar cin kofin Turai ta UEFA guda biyu, inda ya lashe na farko a shekarai dubu biyu da goma 2010 da na karshen a 2012 .

An haife shi a garin Santa Cruz de Tenerife a qasar sipaniya a kulob din San Isidro na gida. Ya zira kwallaye har guda talatin da biyar 35 a kungiyar matasan su a cikin kakar 2003–04, kuma ya buga wa kungiyar farko a Tercera División . [1] A watan Agusta 2004, ya shiga ƙungiyar matasa ta Barcelona . [2]

Pedro ya kasance babban dan wasa ga Barcelona ta yaran na biyu B yayin da kungiyar ta samu ci gaba a cikin shekarai dubu biyu da bakwai zuwa da takwas 2007 – 08 Tercera División, yin wasanni guda talatin da shidda 36 da zira kwallaye har guda shidda shida. A ranar 12 Janairu 2008, ya fara buga wasansa na farko don ƙungiyar farko, yana wasa minti ɗaya a cikin gida 4-0 da Real Murcia a cikin 2007-08 La Liga, amma zai ƙara ƙarin mintuna huɗu kawai a cikin bayyanuwa biyu kacal.

Pedro ya kasance wani babban ɓangare na farkon dan wasa na kakar wasa ta shekarai 2008–09, kuma ya nuna alƙawarin farko, inda ya zura kwallo a ragar Hibernian da New York Red Bulls a qasar amurka bi da bi. A kan sha uku ga watan Agusta shekarai dubu biyu da takwas 2008, ya fara a cikin nasara da suka zura qwallaye hudu da nema 4-0 da Wisła Kraków a zagaye na uku na cancantar 2008-09 UEFA Champions League . Fitowarsa ta farko a matakin rukuni na wannan gasa ya zo ne a ranar sha shidda 16 ga watan Satumba, lokacin da ya maye gurbin Thierry Henry a wasan da ci 3-1 a gida a kan Sporting CP . A kakar wasan cin kofin Barcelona a 2008–09, Pedro ya buga wasanni 14. A wasan karshe na gasar zakarun Turai, ya zo ne a matsayin wanda zai maye gurbinsa a wasan da suka doke Manchester United da ci 2-0 a filin wasa na Olimpico da ke Rome .

  1. Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named LaRendija
  2. Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named Sport