Paulin Pomodimo
Archbishop Paulin Pomodimo (an haife shi ranar 30 ga watan Yunin 1954, a Ziendi) babban limamin Katolika ne a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Shi ne babban Bishop na Archdiocese na Roman Katolika na Bangui, babban birnin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Ya zama babban Bishop a cikin watan Yulin 2003, lokacin da ya maye gurbin Joachim N'Dayen. [1]
Paulin Pomodimo | |
---|---|
mutum | |
Bayanai | |
Jinsi | namiji |
Ƙasar asali | Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya |
Suna | Paulin (mul) |
Shekarun haihuwa | 30 ga Yuni, 1954 |
Harsuna | Faransanci da Harshen Sango |
Sana'a | Catholic priest (en) da Catholic bishop (en) |
Muƙamin da ya riƙe | Archbishop of Bangui (en) , Bishop of Bissangoa (en) , diocesan bishop (en) da Catholic archbishop (en) |
Addini | Cocin katolika |
Consecrator (en) | Joachim N'Dayen, Diego Causero (en) da Michel Marie Joseph Maître (en) |
Ya yi murabus daga muƙaminsa na Archbishop na Bangui a ranar 26 ga watan Mayun 2009 bayan wani bincike na Vatican ya gano cewa yawancin limaman yankin sun karya alƙawarin su na tsafta, talauci da biyayya. [2]
Daga baya shugaba François Bozize ya naɗa shi jami'in kare haƙƙin jama'a na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. [3]