Oba Oloyede Adeyeoba Akinghare ll is the current Arujale Ojima of Okeluse,Ondo State,Nigeria. Shi ne sarkin gargajiya na Okeluse.Adeyeoba wani sarki ne na masarautar Okeluse,karamar hukumar Ose a jihar Ondo.Yana da shekaru sha shida,ya gaji mahaifinsa,Marigayi Oba Akinghare I,Adeyeoba Omomogbe kan karaga a shekarar 2019.Ya sauke karatu daga makarantar sakandare a watan Agusta 2022.

Oloyede Adeyeoba
Rayuwa
Sana'a

A cikin 2022,Oloyede Adeyeoba ya gama karatunsa na sakandare a Greater Tomorrow International College,Arigidi,Ondo,Nigeria. A yanzu haka yana karatun Kimiyyar Siyasa a Jami'ar Afe Babalola don yin Digiri na B.Sc.

Zabi da nadin sarauta

gyara sashe

Ya zama sarki a watan Fabrairun 2019,bayan rasuwar mahaifinsa.An nada shi ya gaji mahaifinsa kasancewar namiji daya tilo da mahaifinsa ya haifa,bisa ga al'adar garinsu,an nada dan sarki na farko a matsayin wanda zai gaje shi.

Rayuwa ta sirri

gyara sashe

Akinghare ll bai yi aure ba amma yana shirin auren mace fiye da ɗaya kamar yadda al'adarsa ta tanada.