Okpa
Okpa (lafazi mai suna Ọkpa) abinci ne da ‘yan kabilar Igbo ke shiryawa da irin wake da ake kira Bambara goro. Ya zama ruwan dare a jihar Enugu kuma an rarraba shi a matsayin abincin gargajiya na Najeriya.Ba Igbo kadai ba;sauran kabilu suna cin shi da pap ko da kanta. Sauran sunayen Igbo na okpa sun hada da ịgba da ntucha.A kasar Hausa ana kiranta da gurjiya ko kwaruru.
Okpa | |
---|---|
pudding (en) | |
Tarihi | |
Asali | Najeriya |
Babban sinadaran da ke cikin okpa sune fulawar Bambara,man dabino,da crayfish. A cikin abinci mai gina jiki,okpa yana da kusan 16.92% ɗanyen furotin,4.93% mai,26.62% carbohydrate da ƙimar kuzari 216.28 kcal,[1] yana mai da shi ɗaya daga cikin madaidaitan ma'auni.