Odette Nyiramilimo (an haife ta a shekarar 1956) likita ce kuma yar majalisar dattawa ta ƙasar Rwanda. Ta yi aiki a matsayin ministar harkokin zamantakewa a gwamnatin Paul Kagame daga watan Maris 2000 zuwa na Oktoban 2003.

Odette Nyiramilimo
Member of the Senate of Rwanda (en) Fassara

Rayuwa
Haihuwa 1956 (67/68 shekaru)
ƙasa Ruwanda
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa da likita

Farkon rayuwa

gyara sashe

Nyiramilimo, yar kabilar Tutsi ce, an haifeta a Kinunu, lardin Gisenyi a 1956. Ita ce ta goma sha bakwai a cikin ‘ya’yan mahaifinta goma sha takwas, wadda matarsa ta biyu ta haifa.

A shekarar 1981 ta kammala karatu a fannin likita a Jami'ar Kasa ta Ruwanda da ke Butare.

Rayuwa ta sirri

gyara sashe

Lokacin da take yar shekara uku an kashe 'yan uwanta da yawa a gwagwarmayar mulki bayan samun 'yancin kai. Ta fuskanci ƙuruciya mai ban mamaki, gami da fuskantar korar ta daga makaranta saboda ita yar kabilar Tutsi ce.

Daga baya ta auri Jean-Baptiste Gasasira, kuma likita ne, su biyun daga baya sun kafa wata sana'a mai zaman kanta ta haihuwa da kuma aikin likitancin yara a Kigali mai suna Le Bon Samaritain (" Good Samaritan ")[1]

An ba da labarin tarihin rayuwarta mai tsawo a cikin littafin Philip Gourevitch Wish to Inform You That Tomorrow We Will Be Killed With Our Families .

Tana da ‘ya’ya 3; Clement Uwajeneza (an haife shi 1980), Ariane Inkesha (an haife shi 1982) da Patrick Cyusa Kinyange (an haife shi a shekara ta 1987)

Ta yi aiki a asibitin Kibuye.[2]

Ta yi aiki a matsayin ministar harkokin zamantakewa a gwamnatin Rwanda daga watan Maris 2000 zuwa Oktoban 2003.

Manazarta

gyara sashe
  1. Republic, The New (2006-07-19). "Q & A: Odette Nyiramilimo". The New Republic. ISSN 0028-6583. Retrieved 2021-11-22.
  2. Republic, The New (2006-07-19). "Q & A: Odette Nyiramilimo". The New Republic. ISSN 0028-6583. Retrieved 2021-11-22.

Hanyoyin hadi na waje

gyara sashe