Obinna
Obinna sunan Igbo ne, ko kuma wani lokacin sunan mahaifi. Asalin sunan ya fito ne daga kabilar Igbo, dake kudu maso gabashin Najeriya, kuma yawanci masu sunan maza ne. Ko da yake mutane daga wasu al'adu suna iya ɗaukar sunan. Fassarar Hausa kai tsaye ita ce,"zuciyar uba". Sunan kuma yana nufin "kursiyin Uba" dangane da mahallin. Wannan ya kara bayyana dalilin da ya sa ake kiran 'ya'yan farko na iyalan Igbo da shi. Fitattun mutane masu sunan sun haɗa da:
Obinna | |
---|---|
sunan gida | |
Bayanai | |
Suna a harshen gida | Obinna |
Tsarin rubutu | Baƙaƙen boko |
Cologne phonetics (en) | 016 |
Sunan da aka ba wa
gyara sashe- Obinna Anyanwu, (an haife shi a shekara ta 1983) mawakin Najeriya kuma marubucin waka, wanda aka fi sani da Waconzy
- Obinna Chidoka (an haife shi a shekara ta 1974), ɗan siyasan Najeriya
- Obinna Ekezie (an haife shi a shekara ta 1975), ɗan wasan ƙwallon kwando na Najeriya
- Obinna Eregbu (an haife shi a shekara ta 1969), ɗan wasan Najeriya
- Obinna Eze (an haife shi a shekara ta 1998) shi ne ɗan wasan ƙwallon ƙafa ta ƙasar Amurka
- Obinna Metu (an haife shi a shekara ta 1988),ɗan wasan Najeriya
- Obinna Nwachukwu (an haife shi a shekara ta 1992), shi ne ɗan wasan ƙwallon ƙafa ta ƙasar Nijeriya
- Obinna Nwaneri (an haife shi a shekara ta 1982), shi ne ɗan wasan ƙwallon ƙafa ta ƙasar Nijeriya
- Obinna Nwosu (an haife shi a shekara ta 1971), ɗan wasan ƙwallon kwando na Najeriya,wanda aka fi sani da Julius Nwosu
- Obinna Oleka (an haife shi a shekara ta 1993), ɗan wasan ƙwallon kwando na Amurka
Sunan mahaifi
gyara sashe- Mikel John Obi (an haife shi John Michael Nchekwube Obinna a shekara ta 1987), ɗan wasan ƙwallon ƙafa ta Najeriya dake bugawa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea.
- Eric Obinna Chukwunyelu (an haife shi a shekara ta 1982) shi ne ɗan wasan ƙwallon ƙafa ta ƙasar Najeriya dake bugawa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta St. George's FC
- Victor Nsofor Obinna (an haife shi a shekara ta 1987), shi ne ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Nijeriya mai buga wa SV Darmstadt shekara 98.
- Ezebuiro Obinna (1947–1999), mawakin Najeriya
Duba kuma
gyara sashe- Obina, laƙabin ɗan wasan ƙwallon ƙafa ta Brazil Manoel de Brito Filho