Nicolas Chumachenco
Nicolas Chumachenco ko kuma Chumachenko (27 Maris 1944 - 12 Disamba 2020) ɗan asalin kasar Poland ne mawakin violin na solo, farfesa, kuma darektan ƙungiyar mawaƙa ta Chambar Sarauniya Sofia.[1] Ya lashe lambar yabo ta Diploma Konex Award a shekarar alif 1999, a matsayin ɗaya daga cikin Mawakan Bow na musamman na tsawon shekaru goma a Argentina.
Nicolas Chumachenco | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Kraków (en) , 27 ga Maris, 1944 |
ƙasa | Poland |
Mutuwa | Schallstadt (en) , 12 Disamba 2020 |
Ƴan uwa | |
Ahali | Ana Chumachenco (en) |
Karatu | |
Makaranta |
Curtis Institute of Music University of Southern California (en) USC Thornton School of Music (en) |
Harsuna | Polish (en) |
Ɗalibai |
view
|
Sana'a | |
Sana'a | violinist (en) |
Kayan kida | goge |
Tarihin Rayuwa
gyara sasheAn haifi Chumachenco a Kraków, a Poland inda sojojin Nazi suka mamaye, ga iyayen ‘yan kasar Ukraine da suka bar Poland a ƙarshen yakin duniya na biyu. Ya girma kuma ya fara koya kiɗa a Argentina . Chumachenco ya bar Argentina don yin karatu a Amurka a Makarantar kiɗa ta Thornton ta Jami'ar Kudancin California tare da Jascha Heifetz sannan daga baya a Cibiyar Curtis da ke Philadelphia tare da Efrem Zimbalist kuma ya sami lambobin yabo a gasar Tchaikovsky ta duniya da gasar kiɗa ta Sarauniya Elisabeth.[2]
Chumachenco ya kasance dan wasan violin na farko a Zurich Quartet, farfesan violin a Hochschule für Musik Freiburg sannan ya yi aiki a matsayin jagora kuma daraktan kiɗa na kungiyar kade-kade ta Sarauniya Sofía Chamber a Madrid .
Ya rasu a Schallstadt, Jamus.
Iyali
gyara sashe'Yar'uwarsa Ana Chumachenco (an haife ta a 1945) farfesa ce itama ta violin a Hochschule für Musik und Theater Munich . Ɗansa Eric Chumachenco (an haife shi a shekara ta 1964) ɗan wasan fiyano ne na gargajiya kuma yana koyarwa a Jami'ar Mozarteum Salzburg.[3]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Nicolás Chumachenco - Concertino Director". Festival Internacional de Música "Ciudad de Ayamonte". Archived from the original on 26 July 2011. Retrieved 4 August 2009.
- ↑ Juan Antonio Torres Planells. "Nicolas Chumachenco, violin". Grijalvo. Retrieved 4 August 2009.
- ↑ "Eric Chumachenco". Mozarteum Salzburg. Archived from the original on 25 September 2020. Retrieved 10 June 2017.